NIN ce kaɗai sahihiyar shaida  a Nijeriya – Sabuwar dokar NIMC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Shaidar ɗan ƙasa ta ƙasa (NIMC) ta sanar da cewa adadin ‘yan Nijeriya da mazauna ƙasar bisa doka da suka yi rajista a Rumbun Bayanai na Shaidar ɗan ƙasa (NIDB) ya haura miliyan 136, yayin da sabuwar Dokar NIMC ta 2026 ta fara aiki a hukumance.

Babbar Darakta Janar ta Hukumar NIMC, Injiniya Abisoye Coker-Odusote, ce ta bayyana hakan yayin wata ziyarar girmamawa da ta kai wa Ma’aikatar Tarayya ta Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki a ranar Litinin.

Ta bayyana cewa, sabuwar dokar ta soke tsohuwar Dokar NIMC ta 2007, tare da shimfiɗa sabon tsarin doka da zai inganta yadda ake tafiyar da tsarin shaidar fasahar zamani na Niieriya. A cewarta, sabuwar dokar ta ƙara tabbatar da cewa Lambar Shaidar ɗan ƙasa (NIN) ita ce kaɗai sahihiyar shaidar asali ta gwamnati ƙarƙashin manufar “Mutum ɗaya, Shaida ɗaya.”

Ta ce, dokar ta tanadi muhimman sauye-sauye da suka haɗa da bai wa NIMC cikakken ikon zama cibiyar tabbatar da ingancin tsarin shaidar fasahar zamani na ƙasa, ƙarfafa kariyar bayanan sirri da tsaron yanar gizo, tare da samar da ingantattun takardun shaida na dijital ga ‘yan ƙasa.

Coker-Odusote ta jaddada cewa gwamnatin tarayya ta ƙuduri aniyar tabbatar da cewa kowane ɗan Nijeriya da duk wani baƙon da ke zaune a ƙasar bisa doka ya samu rajista tare da mallakar lambar NIN cikin ƙanƙanin lokaci. Ta ƙara da cewa, NIMC a shirye take ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki domin amfani da bayanan NIN wajen tsara manufofin tattalin arziki, shirye-shiryen tallafin jama’a da sauran ayyukan ci gaban ƙasa.

Haka kuma ta yaba wa Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, bisa gudunmawar da ya bayar wajen tabbatar da amincewa da sabuwar dokar, tana mai cewa hakan na cikin manufofin Ajandar Sabunta Fata ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Da yake nasa jawabin, Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya bayyana sabuwar Dokar NIMC ta 2026 a matsayin wani gagarumin sauyi da zai ƙarfafa tsarin shaidar dijital da inganta shugabanci a Nijeriya. Sai dai ya yi gargaɗin cewa nasarar dokar za ta ta’allaƙa ne kan yadda za a aiwatar da ita da kuma yadda jama’a za su fara amfana da ita a zahiri.

Ya yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi domin gina amincewar jama’a tare da kawo ƙarshen yawaitar tsarin rajistar shaida iri-iri a hukumomin gwamnati.

Bagudu ya ce, ya zama dole a tabbatar da cewa Lambar NIN ta zama shaidar da za a amince da ita a ko ina cikin ƙasar, domin inganta ayyukan gwamnati, ƙarfafa shugabanci da kuma taimakawa wajen tsara manufofin ci gaban ƙasa bisa sahihan bayanai.

Gwamnati ta bayyana cewa rajistar mutane sama da miliyan 136 na ɗaya daga cikin manyan nasarorin da aka samu tun bayan kafa Hukumar NIMC. A cewar gwamnati, cikakken tsarin amfani da lambar NIN zai taimaka wajen inganta tsare-tsaren kasafin kuɗi da tattalin arziƙi, faɗaɗa damar shiga harkokin banki da hada-hadar kuɗi, ƙarfafa tsaro, rage asarar kuɗaɗen haraji, da kuma inganta rabon tallafin gwamnati da sauran ayyukan jin ƙai.

Yanzu da sabuwar dokar ta fara aiki, ana sa ran Hukumar NIMC za ta ƙara ƙaimi wajen yi wa sauran miliyoyin ‘yan Nijeriya da ba su yi rajista ba rijista domin cika manufar gwamnatin tarayya ta “Mutum ɗaya, Shaida ɗaya.”

By ukarofi