Majalisar Dattawa ta amince da tara tiriliyan N11 a hukumar Kwastom

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kwamitin Majalisar Dattawa Mai Kula da Harkokin Kwastom da Harajin Kaya ya amince da burin tara kuɗaɗen shiga har Naira tiriliyan 11 ga Hukumar Kwastom ta Nijeriya (NCS) a shekarar kasafin kuɗi ta 2026.

Kwamitin ya kuma amince da kasafin kuɗin gudanarwar hukumar na Naira tiriliyan 1.235, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa hukumar za ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da ta fara tare da ƙara yawan kuɗaɗen shiga duk da ƙalubalen tattalin arzikin duniya.

An cimma wannan matsaya ne bayan Babban Kwanturola Janar na Hukumar Kwastom ta Nijeriya, Adewale Adeniyi, ya kare kasafin kuɗin hukumar na shekarar 2026 a gaban kwamitin a harabar Majalisar Dokokin ƙasa.

‘Yan majalisar sun yaba wa Hukumar Kwastom bisa yadda ta zarce burin kuɗaɗen shiga da aka ɗora mata a shekarar 2025, tare da amincewa cewa harkokin kasuwancin ƙasa da ƙasa na fuskantar ƙalubale sakamakon sauye-sauyen tattalin arzikin duniya.

Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa Mai Kula da Harkokin Kwastam da Harajin Kaya, Sanata Isah Jibrin, ya bayyana cewa burin tara Naira tiriliyan 11 yana da girma, amma ana iya cimma shi idan aka ƙara himma.

Ya buƙaci shugabannin Hukumar Kwastom su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da an kai wannan buri. Sanatan ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa tsawaita wa’adin Babban Kwanturola Janar na Hukumar Kwastom, yana mai cewa hakan zai ba shi damar ci gaba da kammala sauye-sauyen da suka fara inganta ayyukan hukumar.

Ya ƙara da cewa, yadda Gwamnatin Tarayya ke ƙara saka hannun jari a manyan ayyukan more rayuwa ya sa ake buƙatar ƙarin kuɗaɗen shiga na cikin gida, lamarin da ya sanya Hukumar Kwastom ta zama ɗaya daga cikin muhimman hukumomin da ke tallafa wa ci gaban ƙasa.

Da yake mayar da martani, Adeniyi ya gode wa Shugaba Tinubu bisa amincewar da ya nuna masa, tare da yaba wa mambobin kwamitin saboda dakatar da hutunsu na majalisa domin sauraron bayanin kasafin kuɗin hukumar.

Yayin da yake nazarin ayyukan hukumar na shekarar 2025, Adeniyi ya bayyana cewa Majalisar Dokokin ƙasa ta amince da burin tara Naira tiriliyan 6.584, amma Hukumar Kwastom ta samu kuɗaɗen shiga har Naira tiriliyan 7.277. A cewarsa, hakan ya zarce burin da aka sanya da Naira biliyan 674.1, wanda ya kai ƙarin kashi 10.24 cikin ɗari.

Ya bayyana cewa an samu wannan nasara ne duk da sauye-sauyen manufofin tattalin arziki da kuma matsalolin tattalin arzikin duniya da suka rage yawan kuɗaɗen shiga.

Daga cikin abubuwan da suka shafi tattara kuɗaɗen shiga akwai dakatar da harajin kayayyakin sadarwa, jinkirin fara aiwatar da Green Taɗ, rangwamen harajin shigo da motoci masu amfani da iskar gas (CNG) da motocin lantarki. Haka kuma ya ce yaƙin Rasha da Ukraine ya ci gaba da kawo cikas ga shigo da wasu muhimman kayayyaki kamar alkama, lamarin da ya shafi kuɗaɗen shiga na Hukumar Kwastom.

Sai dai duk da nasarar da aka samu wajen tara kuɗaɗen shiga, Adeniyi ya ce hukumar ta samu Naira biliyan 808.86 kacal daga cikin kasafin kuɗin gudanarwarta na Naira tiriliyan 1.132 da aka amince da shi a shekarar 2025, wanda ya kai kashi 71.46 cikin ɗari. Game da kasafin shekarar 2026 kuwa, Adeniyi ya bayyana cewa Hukumar Kwastom na sa ran tara jimillar Naira tiriliyan 11.074.

By ukarofi

Leave a Reply