2027: Ko ni ba na tsoron Obi balle Tinubu, inji Umahi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce tsohon ɗan takarar Shugaban ƙasa na Jam’iyyar LP, Peter Obi, ba ya zama barazana ga Shugaba Bola Tinubu ko Jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

Umahi, yayin wata hira da Arise TV a ranar Talata, ya ce bai ma tsoron Obi ba, balle Shugaba Tinubu, yana mai zargin cewa ƙarfin siyasar Obi ya samo asali ne daga yaɗa labarai a kafafen sada zumunta fiye da ainihin tasirinsa.

Ministan ya kuma soki wa’adin shekaru takwas da Obi ya yi a matsayin gwamnan Jihar Anambra, yana zarginsa da kasa gyara hanyoyi, bunƙasa masana’antu da aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa. Saboda haka, ya ce Obi ba shi da hurumin neman Tinubu ya yi murabus.

Haka kuma, Umahi ya zargi magoya bayan Obi da rashin jure ra’ayin da ya saɓa da nasu, yana mai cewa suna cin mutuncin masu suka tare da yi musu barazana.

Da yake kare gwamnatin Tinubu, Umahi ya ce gwamnati ta gaji matsalolin tattalin arziki da suka daɗe suna taruwa, kuma gyaransu ba zai yiwu cikin shekaru uku kacal ba. Ya ƙara da cewa sauye-sauyen da gwamnatin ke aiwatarwa sun fara haifar da sakamako, kuma Tinubu ya cancanci wa’adi na biyu.

By ukarofi