Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Sakkwato a zaɓen 2023, Malam Sa’idu Umar Ubandoma, ya fice daga jam’iyyar ADC tare da komawa APC.
Wannan ma cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko kan yaɗa labarai, Bashar Abubakar, ya fitar.
An ce Sanata Wamakko ne, ya tarɓi Ubandoma zuwa jam’iyyar APC a gidansa da ke Asokoro a Abuja.
Ubandoma, wanda ya taɓa riƙe muƙamin Kwamishinan Kuɗi da kuma Sakataren Gwamnatin Jihar Sakkwato a gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal, ya ce salon jagorancin Sanata Wamakko da ayyukan ci gaban da Gwamna Ahmed Aliyu ke aiwatarwa ne suka ƙarfafa masa gwiwar komawa APC.
Matakin nasa ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan siyasa da mazauna jihar, inda wasu ke yabawa, yayin da wasu ke sukar sauya sheƙarsa.
Tsohon Kwamishinan gwamnatin Tambuwal, Honarabul Abdullahi Hassan, ya bayyana cewa matakin bai dace ba.
A cewarsa, “Ya kamata mutum ya zauna inda ake ƙaunarsa, maimakon ya bar wajen da aka ba shi dama ya koma inda ba a so.”
Ya ƙara da cewa Tambuwal ne ya bai wa Ubandoma dama ta zama kwamishina ba tare da amincewar waɗanda yanzu ya koma cikinsu ba, yana mai cewa hakan ya sa sauya sheƙar tasa ba ta dace ba.
Sai dai Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Sakkwato, Nura Mahe, ya yaba wa matakin Ubandoma, yana mai cewa ficewarsa babbar koma baya ne ga jam’iyyar ADC a jihar.
Shi kuwa mai sharhi kan harkokin siyasa, Muhammad Nasir, ya ce sauya sheƙar ‘yan siyasa ba sabon abu ba ne a Nijeriya, yana mai cewa siyasar aƙida ta ragu sosai.
Ya ce abin da ke jawo suka a wasu lokuta shi ne idan ana kallon sauya sheƙar a matsayin rashin biyayya ga wanda ya tallafa wa mutum.
A cewarsa, “A fahimtata, Ubandoma ya nuna rashin biyayya ga Tambuwal. Tambuwal ne ya kawo shi siyasa, ya ba shi muƙamin.
“Sannan ya tsayar da shi takarar gwamna domin ya gaje shi. Saboda haka, mutane da dama za su ɗauki matakin nasa a matsayin butulci, ba siyasa kawai ba.”
