DSS ta bayyana yadda matar wani da ake zargi da ta’addanci ke sayen harsasai tana kai masa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Jami’in Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Mista Babatunde Afolabi, ya shaida wa Babbar Kotun Tarayya da ke Ibadan cewa Asmau Omar, daya daga cikin wadanda ake tuhuma a shari’ar safarar makamai ba bisa ka’ida ba, na saye tare da kai wa mijinta harsasai a maboyarsa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya tuna cewa Asmau Omar da wasu mutum uku suna fuskantar tuhume-tuhume guda 15 da suka hada da hada baki, safarar harsasai ba bisa ka’ida ba, da kuma taimakawa ayyukan ta’addanci.

Sauran wadanda ake tuhumar sun hada da Olamide Okesola, Emmanuel Olatunji da Adeleke Adewale, wadanda dukkansu jami’ai ne na Hukumar Tsaro da Kariya ta Farar Hula ta Nijeriya (NSCDC).

Dukkan waɗanda ake tuhumar sun musanta zarge-zargen da ake musu tun lokacin da aka gurfanar da su a gaban kotu a shekarar 2023, tare da kin amincewa da gabatar da bayanan da suka bayar ga jami’an tsaro, suna masu zargin cewa an karbe su ne ta hanyar tilastawa.

Sai dai a ranar 3 ga Yuli, Mai Shari’a Nkeonye Maha ta yi watsi da wannan korafi tare da amincewa da bayanan a matsayin hujja a gaban kotu.

Da ake ci gaba da sauraron karar a ranar Litinin, Afolabi ya bayyana wa kotun cewa hukumar DSS ta kama Asmau ne yayin da take kokarin kai wa mijinta makamai da harsasai.

Ya ce, “Yayin da muke ƙowarin cafke Dandake, wanda ake zargi da kasancewa fitaccen ɗan ta’adda da ke addabar jihohin Kwara da Kogi da Oyo da Ogun, mun kama Asmau tana ƙoƙarin kai wa mijinta makamai da harsasai.”

A cewarsa, bayanan sirri da DSS ta samu sun nuna cewa Asmau ta dade tana aikin safarar makamai ga masu aikata ta’addanci.

“An kama ta tare da Buhari Lawan yayin da suke kokarin kai wa mijinta harsasai. Binciken da muka gudanar ya nuna cewa tana da hannu wajen jigilar makamai da harsasai, kuma mun gano tushen samun kayan,” inji shi.

Jami’in DSS ɗin ya ƙara da cewa bayan kama waɗanda ake zargin, an samu harsasai a hannunsu, inda ya gabatar wa kotu da wani faifan bidiyo da ke nuna waɗanda ake tuhuma tare da harsasan a matsayin hujja.

A yayin tambayoyin da lauyoyin bangaren masu kare wadanda ake tuhuma suka yi masa, Afolabi ya bayyana cewa an bayyana mijin Asmau a matsayin fitaccen ɗan ta’adda ne saboda wasu da DSS ta kama a baya sun tabbatar da rawar da yake takawa wajen aikata ta’addanci a yankin Kudu maso Yammacin Nijeriya.

Bayan kammala tambayoyin, lauyan wadanda ake tuhuma, Mista A.B. Ademilua, ya bayyana wa kotun cewa ba zai gabatar da wata kariya ba saboda, a cewarsa, ɓangaren masu gabatar da ƙara bai gabatar da hujjojin da suka isa su tabbatar da zarge-zargen ba.

Lauyan ya ce zai gabatar da bukatar cewa babu wata hujja da za ta sa a ci gaba da shari’ar, tare da neman a ba shi lokaci domin tattara hujjojin da zai jingina da su.

Daga nan ne Mai Shari’a Maha ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 7 ga Oktoba domin ci gaba da shari’ar.

By ukarofi

Leave a Reply