Ruftawar gini ya rutsa da mutane huɗu a Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Aƙalla mutane huɗu ne suka maƙale bayan wani ginin bene mai hawa biyu da ake kan ginawa ya rufta a yankin titin Sultan da ke birnin Kano da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar ranar Juma’a.

Rahotanni sun bayyana cewa, an yi nasarar ceto mutum uku daga ƙarƙashin baraguzan ginin, yayin da ake cigaba da ƙoƙarin ceto mutum na huɗu da al’amarin ya rutsa da su.

Shaidun sun bayyana cewa ma’aikatan ginin sun lura da alamun cewa ginin na shirin ruftawa yayin da suke aiki a bene na sama, lamarin da ya sa suka yi gaggawar tserewa domin tsira.

Sai dai mutane huɗu, ciki har da wani mai gadi da direban adaidaita sahu, sun maƙale lokacin da ginin ya rufta.

Wani daga cikin ma’aikatan ginin, Shu’aibu Yaro, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce injiniyan da ke kula da aikin ya lura da alamun ruftawar ginin, wanda ya sa ma’aikatan suka tsere.

Ya ce, mutum uku, ciki har da mai gadin ginin da wani abokinsa, an ceto su kuma an garzaya da su Asibitin Sir Muhammadu Sanusi da ke Kano domin samun kulawa bayan sun samu raunuka.

By Babaji

Leave a Reply