Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ƙasa (EFCC) ta gurfanar da tsohon Manajan Daraktan Kamfanin Matatar Mai ta Fatakwal (PHRC), Ahmed Dikko, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa tuhume-tuhume 12 da suka shafi zargin wankin kuɗi.
An gurfanar da Dikko tare da kamfanin Masterpiece Projects & Investment Ltd, wanda shi ma ke fuskantar tuhume-tuhume a cikin shari’ar.
A zaman kotun da Mai Shari’a Inyang Ekwo ya jagoranta, Dikko ya musanta dukkanin tuhume-tuhumen da EFCC ta gabatar a kansa, yayin da lauyan kamfanin da ake tuhuma tare da shi ya shigar da ƙin amsa laifi a madadin kamfanin.
EFCC ta zargi tsohon shugaban matatar da amfani da kuɗi kimanin Naira miliyan 218.4 wajen sayen wani gida a yankin Katampe Eɗtension da ke Abuja ba tare da amfani da wata cibiyar kuɗi ba, abin da hukumar ta ce ya saɓa wa dokar hana wankin kuɗi ta shekarar 2022.
Bayan karɓar bayanan ɓangarorin biyu, lauyan Dikko ya roƙi kotu da ta ba wanda yake karewa beli, yana mai cewa ya cika dukkan sharuɗɗan belin da EFCC ta ba shi a matakin bincike.
Sai dai lauyan masu gabatar da ƙara ya buƙaci kotun da ta yi watsi da buƙatar belin, yana mai jingina da hujjojin da hukumar ta gabatar a gabanta.
A hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a Ekwo ya bayyana cewa beli hakki ne da kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada, kuma dole ne a gabatar da ƙwararan hujjoji kafin a hana wanda ake tuhuma samun wannan dama.
Kotun ta amince da bayar da belin Dikko kan kuɗin Naira miliyan 150 tare da mutum guda da zai tsaya masa da irin wannan adadi.
Kotun ta kuma sharɗanta cewa wanda zai tsaya wa Dikko dole ne ya mallaki kadara a yankin da kotun ke da iko a kai tare da gabatar da takardun mallakar kadarar domin tantancewa.
Haka kuma, kotun ta umurci Dikko da ya miƙa fasfo ɗinsa na ƙasa da ƙasa ga kotu tare da hana shi fita daga Nijeriya ba tare da izinin kotu ba.
Mai Shari’a Ekwo ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranakun 12, 13 da 14 ga watan Oktoban 2026 domin fara sauraron shaidu.
Wannan shari’a na zuwa ne makonni kaɗan bayan EFCC ta shigar da ƙorafe-ƙorafe daban-daban kan Dikko da tsohon Manajan Daraktan Matatar Mai ta Warri, Jimoh Yisawu, kan zargin karkatar da kuɗaɗen da aka ware domin gyara da farfaɗo da matatun man gwamnati.
Hukumar ta ce binciken da take gudanarwa kan lamarin ya kai ga gano tare da kwato fiye da Naira biliyan 9.4, dala miliyan 21.2, da kuma kadarori masu yawa a sassa daban-daban na ƙasar nan.
