Hukumar bogi: Ban taɓa zaton haka za ta faru a Nijeriya ba – Kawu Sumaila

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila ya baiyana al’ajabi akan zargin kafa hukumar bogi.

Da ya ke magana a BBC Hausa, Kawu Sumaila ya ce lamarin ya zubar da mutuncin Nijeriya a idon duniya.

Ya kuma baiyana mamaki akan yadda aka saka hukumar ta bogi a kasafin kuɗin Nijeriya, inda ya yi kira ga majalisar dattawan da su yi cikakken bincike don gano ‘yan majalisar da su ke da hannu wajen sake kasafin kudin.

“Abin nan ya fi ƙarfin kai na. Wannan lamari ne da zai zubar da mutuncin Nijeriya a idon duniya. Amma za a iya gano su waye ke da hannu a wannan lamari saboda an saka hukumar a kasafin kuɗi.

“Shi ya sa na ke kira ga abokan aiki na sanatoci dz su yi cikakken bincike akan ya akai ma har hukumar ta samu kasafin kuɗi.

“Wannan ya na da muhimmanci domin tarihi ba a zai manta da mu ba cewa mun yi abinda ya dace ko ba mu yi ba,” inji Sanatan.

By ukarofi