Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Asiya El-Rufai, matar tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ta roƙi Shugaba Bola Tinubu da ya tabbatar an yi wa mijinta adalci, tana mai cewa iyalansu sun bayar da gudunmawa sosai wajen nasarar da ya samu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Asiya ta yi wannan roƙo ne a wani taron manema labarai da ta gudanar tare da ɗaya daga cikin matan El-Rufai, Hajiya Aichatou, a Abuja ranar Talata.
Ta bayyana cewa iyalansu ba sa neman Shugaba Tinubu ya tsoma baki a shari’ar da ake yi wa El-Rufai ko ya hana hukumomin da abin ya shafa gudanar da aikinsu. A cewarta, abin da suke nema kawai shi ne a tabbatar an mutunta haƙƙoƙin mijinta kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya tanada.
”Ya Shugaba, na yi maka kamfe. Na zagaya ƙauyuka da birane a Kaduna ina neman maka ƙuri’a. Mijina ya yi aiki dare da rana domin tabbatar da nasararka. Yanzu abin da muke roƙo shi ne a tabbatar an yi masa adalci kuma a ba shi damar kare kansa cikin ‘yanci,” in ji ta.»
Ta ƙara da cewa suna neman a ba El-Rufai damar ganin likitocinsa, lauyoyinsa da iyalansa ba tare da wani cikas ba, tare da ba shi beli idan ya cika sharuɗɗan da kotu ta gindaya.
“Ba mu ce kada a gurfanar da shi ba. Idan yana da laifi, kotu ta hukunta shi. Idan kuma ba shi da laifi, a sake shi. Amma kada a tauye masa haƙƙoƙin da doka ta ba shi,” in ji Asiya.
Asiya ta ce tun bayan tsare El-Rufai, iyalansu suna rayuwa cikin damuwa saboda halin da yake ciki.
Ta ce mijinta na fama da cututtukan hawan jini da ciwon sukari, kuma suna fargabar cewa rashin samun kulawar lafiya yadda ya kamata na iya jefa rayuwarsa cikin haɗari.
“Mu iyalansa muna kwana muna tashi cikin tsoro. Muna addu’ar kada wata rana mu ji wani labari mara daɗi. Wannan yanayi ya shafi kowa a cikin iyalanmu,” in ji ta.
Kiran na matan El-Rufai ya zo ne bayan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta sanar da kama likitan El-Rufai, Farfesa Bello Abubakar, bisa zargin bayar da bayanan da ba su dace ba dangane da ziyarar jinyar tsohon gwamnan.
Hukumar ta kuma yi zargin cewa El-Rufai ya karya wasu daga cikin sharuɗɗan da kotu ta gindaya masa lokacin da aka ba shi izinin fita domin samun kulawar lafiya. Sai dai lauyoyin El-Rufai sun musanta zarge-zargen, suna masu cewa ana ƙoƙarin tauye masa haƙƙinsa na doka.
Tun bayan kama El-Rufai da Hukumar ICPC a farkon wannan shekarar, lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce a faɗin ƙasar nan.
Hukumar ICPC ta gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kotu kan tuhume-tuhume da suka shafi zargin cin zarafin ofis da kuma wasu harkokin kuɗaɗen gwamnati lokacin da yake mulkin Jihar Kaduna. El-Rufai ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa, yana mai cewa ba su da tushe kuma zai kare kansa a gaban kotu.
Lamarin ya kuma janyo martani daga jam’iyyar ADC da wasu ƙungiyoyin siyasa, waɗanda suka yi zargin cewa ana amfani da hukumomin gwamnati wajen matsa wa tsohon gwamnan lamba. Sai dai gwamnatin tarayya da ICPC sun sha nanata cewa shari’ar ba ta da alaƙa da siyasa, kuma ana gudanar da ita ne bisa tanadin doka.
