Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Zuriyar Alhaji Muhammad Sulaiman Maizaure Matazu ta gudanar da gagarumin taron sada zumunci da ya haɗa ‘ya’ya, jikoki da sauran ‘yan uwa daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
Taron ya gudana ne a ranar Lahadi a gidan Mumbayya da ke jihar Kano.
Shugaban zuriyar, Malam Auwalu Umar Matazu, ya ce babban manufar taron ita ce ƙarfafa zumunci da haɗin kai tsakanin ‘yan uwa da kuma tabbatar da ci gaba da kyawawan al’adun iyali.
Shi ma sakataren ƙungiyar, Malam Naziru Umar Matazu, tare da Alhaji Tijjani Umar Matazu, sun yabawa kyakkyawan tarbiyya da shugabancin da suka gada daga kakanninsu.
Sun bayyana marigayi Muhammad Sulaiman Maizaure Matazu a matsayin malami, manomi, ɗan kasuwa kuma mutum mai taimakon al’umma.
