Yankuna 1,402 cikin jihohi 28 na fuskantar matsananciyar barazanar ambaliya – Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta sake yin gargaɗi kan yiwuwar aukuwar ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na ƙasar nan, inda ta bayyana cewa al’ummomi 1,402 da ke jihohi 28 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja na fuskantar barazanar ambaliya tsakanin ranar 5 zuwa 18 ga Yulin 2026.

Gargaɗin na ƙunshe ne cikin sabon rahoton hasashen ambaliya da Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, ta hannun Cibiyar Gargaɗin Farko Kan Ambaliya ta ƙasa, ta fitar. Rahoton ya nuna cewa ana sa ran ci gaba da samun ruwan sama mai ƙarfi a wannan lokaci, lamarin da ka iya haddasa ambaliyar da za ta iya jawo asarar rayuka, lalata dukiyoyi da kuma shafar muhimman ababen more rayuwa.

A cewar rahoton, al’ummomi 987 da ke cikin jihohi 21 an sanya su cikin yankunan da ke fuskantar matsananciyar barazanar ambaliya, yayin da wasu al’ummomi 415 a jihohi bakwai da Babban Birnin Tarayya aka sanya su cikin yankunan da ke buƙatar sa ido na musamman saboda haɗarin ambaliya.

Ma’aikatar ta bayyana cewa an yi hasashen ne bisa nazarin yanayin ruwa da yanayi, hasashen yawan ruwan sama, alamomin haɗarin ambaliya da kuma tantance irin raunin da al’ummomi ke da shi, waɗanda suka nuna cewa akwai babban yiwuwar ambaliya a yankuna da dama.

Jihohin da aka sanya cikin rukunin da ke fuskantar babbar barazana sun haɗa da Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Benuwe, Kuros Riba, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Imo, Kogi, Kwara, Legas, Neja, Ogun, Ondo, Osun, Oyo da Ribas.

Rahoton ya kuma nuna cewa manyan biranen da ake sa ran za su fi fuskantar haɗarin ambaliya sun haɗa da Legas, Fatakwal, Benin City, Kalaba, Warri, Aba, Umuahia, Owerri, Enugu, Makurdi, Lokoja, Asaba, Uyo, Yenagoa, Akure, Abeokuta, Ibadan, Osogbo, Awka da Onitsha.

Haka kuma, Adamawa, Babban Birnin Tarayya (Abuja), Kebbi, Kogi, Kwara, Neja da Taraba na cikin yankunan da daruruwan al’ummomi za su iya fuskantar mummunar ambaliya idan ruwan saman ya ƙaru fiye da yadda aka yi hasashe.

Rahoton, wanda Daraktan Sashen Kula da Zaizayar ƙasa, Ambaliya da Yankunan Gabar Ruwa, Usman Abdullahi Bokani, ya sanya wa hannu, ya buƙaci mazauna yankunan da ke cikin haɗari da su ɗauki matakan kariya cikin gaggawa domin rage illar da ambaliyar ka iya haifarwa.

Ma’aikatar ta shawarci al’umma da su tantance wuraren da za su iya tserewa idan ambaliya ta taso, su kwashe masu rauni zuwa wurare masu aminci idan ya zama dole, su guji zama a bakin koguna da yankunan da ke ƙasa, tare da kasancewa cikin shiri a duk tsawon lokacin da gargaɗin ya shafa.

Har ila yau, ta umarci Hukumomin Ba da Agajin Gaggawa na Jihohi (SEMA), ƙananan hukumomi, jami’an kula da muhalli da wakilan sa ido kan ambaliya a matakin al’umma da su ƙara sa ido a kan koguna, magudanan ruwa, gadoji, bututun ruwa da yankunan da zaizayar ƙasa ke barazana domin gano duk wata matsala cikin lokaci.

An kuma buƙaci al’ummomin da ke cikin yankunan da aka sanya cikin rukunin haɗari da su share magudanan ruwa da suka toshe, su rika sa ido kan rafuka da koguna, su kai rahoton duk wani hauhawar ruwa da ba a saba gani ba, tare da ci gaba da hulɗa da Cibiyar Gargaɗin Farko Kan Ambaliya ta ƙasa. Gwamnatin Tarayya ta kuma yi kira ga gwamnatocin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki da su riƙa tura rahotannin da suka tattara daga filin aiki kan ambaliya domin taimakawa wajen sa ido da kuma inganta hasashen ambaliya a nan gaba.

Wannan sabon gargaɗi na zuwa ne bayan jerin irin waɗannan sanarwar da gwamnatin tarayya ta fitar tun bayan fara daminar bana, lamarin da ke nuna cewa yankunan da ke fama da ambaliya na iya sake fuskantar ƙalubale idan ba a ɗauki matakan kariya da wuri ba.

By ukarofi