Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙaryata raɗe-raɗi da rahotanni masu yayata cewa ya sanar da daina amfani da takardar Naira 100 ta ainihi.
Cikin wata sanarwar da CBN ya fitar a ranar Laraba, 8 ga Yuli 2026, mai ɗauke da sa hannun Daraktar Riƙo ta Sashen Hulɗa da Jama’a da Sadarwa, Hajiya Hakama Sidi Ali, bankin ya yi ƙarin haske kan matsayin takardar kuɗin Naira
N100 a matsayin halastacciya abin ci gaba da karɓa da yin hada-hadar kuɗin biyan buƙatun yau da kullum.
Kan haka, CBN ya ja hankalin jama’a kan su yi watsi da rahotannin da ke nuna cewa wasu daga cikin jama’a, ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki suna ƙin karɓar tsohuwar takardar kuɗin Naira 100, bisa zargin cewa ta daina kasancewa halastacciyar takardar kuɗi.
Domin kawar da duk wata shakka, CBN yana sake jaddada cewa takardar kuɗin Naira 100 ta musamman, wadda aka fito da ita daga baya da kuma takardar kuɗin Naira 100 ta yau da kullum, wato wancan ta farko, har yanzu halastattun takardun kuɗi ne a Nijeriya, kuma dole ne a karɓe su wajen dukkan mu’amaloli a faɗin Nijeriya.
“Takardar Naira 100 ta musamman, wadda aka fitar domin bikin cika shekaru 100 da kafuwar Nijeriya, ba ta maye gurbin tsohuwar takardar N100 ta yau da kullum ba.
“CBN na gargaɗin mutane, ‘yan kasuwa, cibiyoyin kuɗi da sauran masu gudanar da harkokin tattalin arziki cewa kada su ƙi karɓar takardar kuɗin Naira 100 ta yau da kullum. Domin yin hakan ya saɓa wa tanade-tanaden Dokar CBN kuma yana raunana amincewar jama’a da kuɗin ƙasar nan.”
CBN ya yi gargaɗin cewa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar matakan dokar da suka dace kan duk wani mutum ko hukuma da aka samu da laifi ba.
“CBN ya ci gaba da jajircewa wajen kare mutuncin Naira, tabbatar da amincewa da dukkan takardun kuɗi da aka fitar bisa doka, tare da inganta zagayawar kuɗi cikin sauƙi a faɗin Nijeriya.”
Sanarwar ta ci gaba da yin bayani cewa, “ana kira ga dukkan ‘yan Nijeriya su riƙa karɓa tare da gudanar da mu’amala da dukkan takardun kuɗin da Babban Bankin Nijeriya ya fitar bisa doka.”
Domin samun ƙarin bayani, an kuma shawartar jama’a da su tuntuɓi CBN ta hanyoyin sadarwar hukuma na bankin.
