Amurka ta bayyana sunayen ’yan Nijeriya 124 za ta koro saboda laifuka

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin ƙasar Amurka ta fitar da sabon jerin sunaye da hotunan ’yan Nijeriya 124 da ta sanya cikin rukunin waɗanda ta bayyana a matsayin “manyan masu laifi mafi muni”, a wani ɓangare na sabon matakin da gwamnatin Donald Trump ke ɗauka na tsaurara dokokin shige da fice da korar baƙi.

Rahoton ya nuna cewa Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka (DHS) ce ta wallafa jerin a shafinta na hukuma a ranar Laraba, inda ta bayyana cewa mutanen da aka sanya sunayensu ba ’yan ƙasar Amurka ba ne, kuma Hukumar Shige da Fice da Kwastom ta Amurka (ICE) na shirin korarsu daga ƙasar.

Sai dai hukumar ba ta bayyana ranar da za a fara korar mutanen ba, duk da cewa ta ce matakin na daga cikin ci gaba da aiwatar da dokokin shige da fice kan mutanen da aka samu da aikata manyan laifuka.

Haka kuma, DHS ba ta fayyace irin laifukan da ake zargin kowanne daga cikin mutanen ya aikata ba, ko kuma lokacin da za a aiwatar da hukuncin korarsu.

A cikin sanarwar da ta fitar tare da jerin sunayen, hukumar ta ce: “Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka na bayyana sunayen mafi munin masu laifi daga cikin baƙin da jami’an ICE suka kama. A ƙarƙashin jagorancin DHS, jami’anmu na cika alƙawarin Donald Trump na korar baƙi masu laifi daga ƙasar, inda aka fara da wacanda suka fi hatsari.”

Matakin na daga cikin manufofin shige da fice da gwamnatin Trump ta ƙaddamar bayan dawowarsa kan mulki a ranar 20 ga Janairu, 2025.

A ranar farko da ya koma Fadar White House, Trump ya rattaba hannu kan wasu umarnin shugaban ƙasa da suka ayyana shige da ficen ba bisa ƙa’ida ba a matsayin gaggawar tsaron ƙasa, tare da umartar hukumomin tarayya su ƙarfafa tsaron iyakoki da kuma hanzarta korar baƙin da ba su da takardun zama.

ɗaya daga cikin umarnin, mai taken “Kara Al’ummar Amurka Daga Mamaya”, ya umurci hukumomin shige da fice su bai wa kama da korar baƙin da ake iya fitarwa daga ƙasar fifiko, musamman waɗanda ake ganin barazana ce ga tsaron jama’a da na ƙasa.

Mai magana da yawun Fadar White House, Karoline Leaɓitt, ta kare wannan mataki, tana mai cewa gwamnatin Trump ta ƙuduri aniyar aiwatar da dokokin shige da fice tare da korar baƙin da ba su da takardu, musamman masu tarihin aikata manyan laifuka.

Bayanan gwamnatin Amurka sun nuna cewa tun bayan fara wannan sabon shiri, ƙasashen Guatemala, Honduras, Mexico da El Salvador ne suka fi yawan mutanen da aka kora, yayin da kuma aka faɗaɗa jigilar waɗanda ake kora zuwa ƙasashen Afirka, Asiya da yankin Caribbean.

A baya-bayan nan ma, Nijeriya ta shiga sahun ƙasashen da gwamnatin Trump ta tsaurara wa matakan biza, inda a watan Yuni ta sanya takunkumin biza kan wasu ’yan Nijeriya, tana mai danganta hakan da matsalolin tantance bayanan shaida, musayar bayanai, yawaitar zama fiye da wa’adin biza da kuma batutuwan tsaro.

Hukumar DHS ta kuma bayyana cewa ta wallafa hotuna da bayanan mutanen da ke cikin sabon rajistar domin tallafa wa shirin korarsu daga Amurka.

Cikakken jerin sunayen ’yan Nijeriya da DHS ta wallafa:

Sunday Adediora, Sunday Kunkushi, Mkpouto Etukudoh, Marcus Unigwe, Olaniyi Ojikutu, Boluwaji Akingunsoye, Ejike Asiegbunam, Emmanuel Mayegun Adeola, Bamidele Bolatiwa, Ifeanyi Nwaozomudoh, Aderemi Akefe, Solomon Wilfred, Chibundu Anuebunwa, Joshua Ineh, Usman Momoh, Oluwole Odunowo, Bolarinwa Salau, Oriyomi Aloba, Oludayo Adeagbo, Olaniyi Akintuyi, Talatu Dada, Olatunde Oladinni, Jelili ƙudus, Abayomi Daramola, Toluwani Adebakin, Olamide Jolayemi, Isaiah Okere, Benji Macaulay, Joseph Ogbara, Olusegun Martins, Kingsley Ariegwe, Olugbenga Abass, Oyewole Balogun, Adeyinka Ademokunla, Christian Ogunghide, Christopher Ojuma, Olamide Adedipe, Patrick Onogwu, Olajide Olateru-Olagbegi, Omotayo Akinto, Kenneth Unanka, Jeremiah Ehis, Oluwafemi Orimolade, Ayibatonye Bienzigha, Uche Diuno, Akinwale Adaramaja, Boluwatife Afolabi, Chinonso Ochie, Olayinka A. Jones, Theophilus Anwana, Aishatu Umaru, Henry Idiagbonya, Okechukwu Okoronkwo, Daro Kosin, Sakiru Ambali, Kamaludeen Giwa, Cyril Odogwu, Ifeanyi Echigeme, Kingsley Ibhadore, Suraj Tairu, Peter Eƙuere, Dasola Abdulraheem, Adewale Aladekoba, Akeem Adeleke, Bernard Ogie Oretekor, Abiemwense Obanor, Olufemi Olufisayo Olutiola, Chukwuemeka Okorie, Abimbola Esan, Elizabeth Miller, Chima Orji, Adetunji Olofinlade, Abdul Akinsanya, Elizabeth Adeshewo, Dennis Ofuoma, ƙuazeem Adeyinka, Ifeanyi Okoro, Oluwaseun Kassim, Olumide Bankole Morakinyo, Abraham Ola Osoko, Oluchi Jennifer, Chibuzo Nwaonu.

By ukarofi