Kotu ta tsare tsohon Shugaban kotun ɗa’ar Ma’aikata, Danladi Umar a Kuje

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya Abuja da ke zama a Maitama, Abuja, ta bayar da umarnin tsare tsohon shugaban Kotun ɗa’a ta Jami’an Gwamnati (CCT), Danladi Umar, a Gidan Gyaran Hali na Kuje har sai an saurari buƙatar belinsa.

Hukuncin ya fito ne daga bakin Mai Shari’a Peter Kekemeke bayan Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar da Umar bisa tuhume-tuhume huɗu da suka shafi zargin amfani da muƙaminsa wajen bai wa kansa wata fa’ida da ba ta dace ba yayin da yake jagorantar Kotun ɗa’a ta CCT.

A lokacin da aka karanta masa tuhume-tuhumen, Danladi Umar ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa.

Lauyan EFCC, Christopher Mshelia, ya buƙaci kotu ta sanya ranar fara shari’a tare da umartar a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma har zuwa lokacin da za a fara sauraron shari’ar.

Sai dai lauyan Danladi Umar ya sanar da kotun cewa tuni ya shigar da buƙatar beli, yana roƙon kotun ta saurare ta nan take.

EFCC ta nuna adawa da hakan, tana mai cewa ba da jimawa ba aka ba ta kwafin buƙatar belin, don haka tana buƙatar lokaci domin nazari da gabatar da martaninta.

Bayan sauraron ɓangarorin biyu, Mai Shari’a Kekemeke ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 15 ga Yuli, domin yanke hukunci kan buƙatar belin, tare da umartar a ci gaba da tsare Danladi Umar a Gidan Gyaran Hali na Kuje har zuwa lokacin.

By ukarofi

Leave a Reply