*Ku harbi ’yan ta’adda babu jiran umarninmu – Musa ga dakaru
*Ya ce, za a ɗauki sojan da ya jira umarnin harbi tamkar ɗan ta’adda
*Majalisa ta nemi dakatar da shirin gyaran halin ’yan ta’adda
*Kwamandojin ISWAP shida da iyalansu sun miƙa wuya a Borno
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya umarci dakarun Rundunar Sojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro su riƙa ɗaukar mataki kai tsaye kan duk wani ɗan bindiga ko ɗan ta’adda da suka ci karo da shi, yana mai gargaɗin cewa duk jami’in da ya ƙi buɗe wuta saboda jiran umarni daga manyansa za a ɗauke shi tamkar mai haɗa baki da masu aikata laifin.
Janar Musa ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Sakkwato yayin rabon sabbin motocin sulke ga hukumomin tsaro, inda ya sake jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa da kuma murƙushe matsalolin rashin tsaro. Yayin da yake jawabi ga jami’an tsaro, Ministan ya ce duk sojan da aka tura yankin aiki yana da cikakken alhakin tunkarar ’yan bindiga da ’yan ta’adda ba tare da jiran wani sabon umarni ba.
“Ina so na sake jaddada wa dukkan jami’an Rundunar Soji da sauran hukumomin tsaro cewa da zarar an tura ku bakin aiki, kada ku jira wani umarni kafin ku harbi ɗan bindiga ko ɗan ta’adda. Ina faɗin wannan a sarari. Duk wanda ya ƙi harbin ko kashe ɗan bindiga ko ɗan ta’adda saboda yana jiran umarni, za mu ɗauke shi tamkar ɗan bindiga,” inji shi.
Ministan ya tunatar da jami’an tsaro cewa makamai, motocin sulke da sauran kayan aikin da aka ba su an saya ne da kuɗaɗen harajin ’yan Nijeriya, don haka wajibi ne su yi amfani da su yadda ya kamata wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya ce, kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya, gwamnatocin jihohi, ƙananan hukumomi da masu biyan haraji suka bayar ne aka yi amfani da su wajen sayen waɗannan kayan aiki domin murƙushe duk wanda ke ƙoƙarin haddasa tashin hankali a ko ina cikin ƙasar.
A cewarsa, alhakin jami’an tsaro ne su kawar da masu aikata laifuka kafin su zama barazana ga jami’an tsaron ko al’umma.
Sai dai Janar Musa ya bayyana cewa duk da muhimmancin makamai da kayan yaƙi, ba su kaɗai za su iya samar da zaman lafiya mai ɗorewa ba.
Ya ce samun nasara a yaƙi da rashin tsaro na buƙatar ƙwarewa, bin ƙa’idojin aiki, amfani da sahihan bayanan sirri da kuma cikakken haɗin gwiwa tsakanin dukkan hukumomin tsaro.
Haka kuma ya yi kira da a ƙara ƙarfafa haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da al’ummomin yankuna, yana mai cewa bayanan sirrin da mazauna yankuna ke bayarwa na taka muhimmiyar rawa, domin masu aikata laifuka na rayuwa ne a cikin al’umma.
Ya ce, ba za a samu tsaro mai ɗorewa ba sai da goyon bayan sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, shugabannin al’umma da sauran jama’a.
Ministan ya ƙara da cewa idan aka samu cikakken haɗin kai tsakanin jama’a da hukumomin tsaro, zai yi matuƙar wahala ga ’yan ta’adda da ’yan bindiga su ci gaba da gudanar da ayyukansu.
Har ila yau, ya umarci jami’an tsaro da su kula da sabbin motocin sulken da aka raba musu, yana mai bayyana su a matsayin manyan kadarorin ƙasa da aka saya da biliyoyin nairori.
Ya ce, gwamnati za ta duba yadda aka kula da motocin bayan shekara guda domin tabbatar da cewa ba a yi sakaci da su ko aka lalata su ba.
A ƙarshe, Janar Musa ya tabbatar wa al’ummar Jihar Sakkwato da sauran ’yan Nijeriya cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ɗaukar matakan inganta tsaron ƙasa ta hanyar kyautata walwalar jami’an tsaro, inganta tattara bayanan sirri, saka hannun jari a fasahar zamani, ƙarfafa haɗin gwiwar hukumomin tsaro da kuma samar da isassun kayan aikin gudanar da ayyuka.
Majalisar Wakilai ta buƙaci a dakatar da shirin gyaran halin tubabbun ’yan ta’adda:
Majalisar Wakilai ta Tarayya ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da shirin gyara hali da mayar da tubabnun ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da ’yan bindiga cikin al’umma, yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan taɓarɓarewar tsaro da kuma yawaitar biyan kuɗin fansa a ƙasar.
Matsayar ta biyo bayan amincewar majalisar da wani ƙuduri da ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Shomolu ta Jihar Legas, Ademorin Kuye, ya gabatar a zaman majalisar na ranar Laraba.
Yayin gabatar da ƙudurin, Kuye ya buƙaci gwamnatin tarayya ta rushe abin da ya bayyana a matsayin tattalin arzikin kuɗin fansa, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tattara bayanan sirrin kuɗi da kuma tabbatar da cikakken aiwatar da dokokin yaƙi da halasta kuɗaɗen haram.
Ya ce, rahotannin da Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) da wasu cibiyoyin binciken tsaro masu zaman kansu suka fitar sun nuna cewa ’yan Nijeriya sun biya kimanin Naira tiriliyan 2.23 a matsayin kuɗin fansa tsakanin Janairun 2021 zuwa Yunin 2025.
A cewarsa, binciken da Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta ƙasa, ƙarƙashin Ofishin Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA), ya gudanar ya gano cewa masu gudanar da harkokin POS da wasu hanyoyin hada-hadar kuɗi na taimakawa wajen biyan kuɗin fansa da kuma ɓoye hanyoyin zirga-zirgar kuɗin, abin da ke hana bincike da dawo da kuɗaɗen cikin sauƙi.
Kuye ya ƙara da cewa ƙungiyoyin ta’addanci da masu aikata laifuka na amfani da hanyoyin hada-hadar kuɗi na hukuma da na bayan fage, ciki har da masu canjin kuɗi, dandamalin kuɗaɗen Crypto, cinikin dabbobi da sauran dabarun babaƙalar kuɗi domin ɓoye kuɗaɗen da suka samu daga fansa.
Ya yi gargaɗin cewa raunin musayar bayanan sirrin kuɗi da rashin cikakken aiwatar da dokokin hana halasta kuɗaɗen haram na ƙara ta’azzara matsalar tsaro, yana rage amincewar jama’a ga gwamnati tare da ƙara yiwuwar Nijeriya ta fuskanci takunkumai daga ƙasashen duniya, ciki har da ci gaba da kasancewa cikin jerin sa-ido na FATF.
Sai dai ƙudurin ya haifar da muhawara a majalisar, inda Shugaban Kwamitin Kula da Asusun Jama’a na Majalisar Wakilai, Bamidele Salam, ya nuna adawa da batun haramta biyan kuɗin fansa.
Ya ce bai dace a ɗora wa waɗanda suka biya kuɗin fansa laifi ba, matuƙar gwamnati ba ta tabbatar da cikakken kariyar rayuka da dukiyoyin al’umma ba.
A nasa ɓangaren, Shugaban Kwamitin Sojojin Ruwa na Majalisar Wakilai, Yusuf Gagdi, ya goyi bayan ƙudurin, yana mai cewa biyan kuɗin fansa na ƙara ƙarfafa masu garkuwa da mutane da ’yan bindiga wajen ci gaba da aikata laifukansu.
Daga nan ne ya gabatar da gyara ga ƙudurin, inda ya buƙaci gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin gyara hali da sake haɗa tsoffin ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da ’yan bindiga cikin al’umma.
Hon. Gagdi ya ce duk wanda ya kashe mutane da gangan bai cancanci a bar shi ya rayu ba, yana mai cewa waɗanda ke kai farmaki gidajen jama’a, su yi garkuwa da su, su azabtar da su kafin kashe su, ciki har da sarakunan gargajiya, ba su cancanci wata sassauci ba.
Ya kuma yi zargin cewa wasu daga cikin tsoffin mayaƙan da aka gyara halinsu na iya kasancewa suna bai wa ƙungiyoyin ta’addanci bayanan sirri, lamarin da ke taimaka musu kai hare-hare kan jami’an tsaro.
Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya gabatar da gyaran ƙudurin domin kaɗa ƙuri’ar murya, inda ’yan majalisar suka amince da shi baki ɗaya.
Shi ma ɗan majalisar mai wakiltar Damboa/Gwoza/Chibok a Jihar Borno, Ahmadu Jaha, ya ce iyalan waɗanda aka taɓa yin garkuwa da su ne kaɗai za su iya fahimtar irin raɗaɗin da lamarin ke haifarwa.
Ya tambayi waɗanda ke adawa da biyan kuɗin fansa ko za su ci gaba da wannan matsaya idan ɗaya daga cikin ’yan uwansu ya faɗa hannun masu garkuwa da mutane.
Wannan mataki na Majalisar Wakilai ya zo ne kwana guda bayan Majalisar Dattawa ita ma ta buƙaci gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin gyaran hali da sake haɗa tsoffin mayaƙan Boko Haram cikin al’umma.
An ƙaddamar da shirin gyaran halin tsoffin ’yan ta’adda ne a shekarar 2016 ƙarƙashin shirin soja mai suna Operation Safe Corridor, domin sauya tunanin waɗanda suka miƙa wuya daga ƙungiyoyin ta’addanci tare da mayar da su cikin al’umma.
Yadda kwamandojin ISWAP shida da iyalansu sun miƙa wuya a Borno:
Dakarun Bataliyar Sojoji ta 192 ƙarƙashin Sashe na 1 na Rundunar Operation Haɗin Kai sun samu gagarumar nasara bayan da wasu kwamandojin ƙungiyar ISWAP shida tare da iyalansu suka miƙa wuya a Jihar Borno.
Sanarwar da Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar a ranar Laraba ta bayyana cewa, wannan na daga cikin jerin nasarorin da sojoji suka samu a yankin, ciki har da ceto mutanen da aka sace, cafke masu kai wa ‘yan ta’adda kayan aiki, ƙwato kuɗaɗe, makamai da miyagun ƙwayoyi, tare da fatattakar wani hari da mayaƙan ISWAP suka kai.
A cewar rundunar, an samu sama da Naira miliyan 1.5, wayoyin hannu ƙirar Tecno guda biyu da sauran kayayyaki daga hannun waɗanda suka miƙa wuya.
Haka zalika, dakarun Bataliya ta 115 sun ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Askira/Uba ta Borno, inda suka kuma ƙwato Naira miliyan 1.2 da ake zargin kuɗin ayyukan ta’addanci ne, tare da kayan abinci da sauran kayayyakin tallafa wa ‘yan ta’adda.
Tuni aka kai waɗanda aka ceto wurin da ake kula da lafiyarsu tare da ba su tallafin jinya da na shawarwari.
A wani samame kuma, dakarun sun daƙile wani hari da ISWAP ta kai kan wani sansanin soji a Borno. Duk da cewa mayaƙan sun kutsa zuwa wani ɓangare na sansanin na ɗan lokaci, sojojin sun sake tattaruwa, suka ƙaddamar da farmaki, suka fatattake su tare da yi musu mummunar asara.
Sai dai rundunar ta tabbatar da rasuwar soja guda ɗaya yayin artabun, yayin da motocin yaƙi guda biyu da wasu kayan aiki suka lalace. Rundunar ta ce, har yanzu sansanin FOB Logomani na ƙarƙashin cikakken ikon dakarunta, inda aka tura ƙarin sojoji kuma ake ci gaba da sintiri domin ƙarfafa tsaron yankin.
A Jihar Adamawa kuwa, dakarun Bataliya ta 232 sun kama wani fitaccen da ake zargi da aikata manyan laifuka a ƙaramar hukumar Gombi. Binciken da aka ci gaba da yi ya kai ga ƙwato bindigar AK-47 guda ɗaya, mujallu biyu da harsasai 28.
Haka kuma, dakarun Bataliya ta 149 sun cafke mutane biyu da ake zargin suna kai wa ‘yan ta’adda kayan tallafi a ƙaramar hukumar Mobbar ta Borno. An ƙwato kuɗi, mota ƙirar ɓolkswagen Golf, kayan gini, kayan amfanin gida da sauran kayayyakin da ake zargin an tanade su ne domin mayaƙan ta’adda.
A wani samame na daban, dakarun Briged ta 24 tare da haɗin gwiwar Rundunar Tsaro ta Fararen Hula (CJTF) sun kai farmaki maboyar ‘yan ta’adda a yankin Wulgo, inda suka ƙwato buhun da ke ɗauke da miyagun ƙwayoyi bayan ‘yan ta’addan sun tsere.
Har ila yau, sojoji sun kama wani da ake zargi da kai wa Boko Haram/ISWAP kayan tallafi a shingen bincike na Molai, yayin da yake ɗauke da tarin magunguna ba tare da izini ba.
A yankin Sashe na 2, dakarun Bataliya ta Tankoki ta 233 tare da mafarauta sun kama wani mutum daga ƙauyen Ngirya a ƙaramar hukumar Tarmuwa ta Jihar Yobe da tayoyin babura guda biyar da ake zargin zai kai wa ‘yan ta’adda.
Rundunar Operation Hadin Kai ta ce waɗannan nasarori sun nuna tasirin ci gaba da kai farmaki, samun ingantattun bayanan sirri da kuma haɗin gwiwar jami’an tsaro wajen tarwatsa hanyoyin samar wa ‘yan ta’adda kayan aiki da kare al’ummomin Arewa maso Gabas.
Ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da aikin ceto har sai an kuɓutar da duk mutanen da aka yi garkuwa da su, tare da yin gargaɗin cewa duk wanda aka kama yana kai wa ‘yan ta’adda abinci, mai, kayan gini, sufuri ko wata irin gudunmawa, zai fuskanci hukunci bisa tanadin doka.
