Sojoji sun daƙile hari a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Sojojin Nijeriya da ke aikin samar da tsaro a kan hanyar da ta haɗa Nijeriya da Jamhuriyar Benin sun fatattaki wani ayarin mahara da suka suka kai farmaki a garin Ka’oje da ke ƙaramar hukumar Bagudo cikin daren Larabar nan.

Malam Nuhu Ka’oje ya shaida wa waƙilin blueprint Manhaja da cewa maharan sun shigo garin Ka’oje ne da misalin ƙarfe biyu na dare kan babura inda suka yi arba da sojojin.

Ya ƙara da cewa maharan ana sa ran masu garkuwa da mutane ne domin neman kuɗin fansa saboda sau da yawa sukan shiga cikin gari su ɗauki mutane su gudu da su.

By ukarofi

Leave a Reply