Sojoji sun kashe ‘yan bindiga takwas a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Sojojin 17 Bridge sun sami nasarar kashe ‘yan bindiga takwas tare da ƙwace bindiga ƙirar AK 47 a ƙaramar hukumar Bakori da ke Jihar Katsina.

Kamar yadda jami’in yaɗa labarai na rundunar 17 Bridge Kaftin Abayomi Adisa ya fitar da sanarwa, wannan lamari ya biyo bayan bayanan sirri da wani na kusa da hannun ƙasurgumin ɗan bindiga Idi Abasu Aiki cewa suna ƙoƙarin datse hanyar Kakumi zuwa Guda da nufin kai hari da matafiya hanyar.

Da jin haka a cewar sojoji suka isa hanyar da ‘yan bindigan suka tare nan sojojin suka shiga bata kashi da ‘yan bindigan har suka ga kashe mutane takwas da ƙwato bindiga ƙirar AK 47 da buburan hawa guda biyar.

Bayan da ƙura ya lafa sai sojoji suka sami labarin ‘yan bindiga suna shirin ɗaukar fansa ga alummar Guga, Unguwar Dan Shauyi da ƙwai da wasu ƙauyukan da ke maƙwabtaka da su ,sai nan take rumfunar sojojin suka tura jami’an su da ke sansanin Ruwan Godiya da Mabai domin gudanar da sunturi a yankin.

Kaftin Abayomi ya bayyana cewa sojoji na sanya ida tare da zaman cikin shi ko da ta kwana a yankin.

By ukarofi

Leave a Reply