
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban alƙalan wasa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa-da-Ƙasa (FIFA), Pierluigi Collina ya yi tir da babban murya akan zarge-zargen Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Misra da Koci Hossam Hassan bayan Argentina ta yi nasara akan ƙasar da ci 3 da 2 a wasan zagayen ‘yan 16 na gasar Kofin Duniya da ke cigaba da gudana a Nahiyar Amurka.
Misra ta shigar da ƙara ne akan alƙalin wasa François Letexier a game da ƙwallon da aka soke da kuma hana ‘yan wasanta buga fenareti yayin da ake gwabzawa tsakaninta da Argentina.

“Lallai sun so su bar wadda ta lashe kofin a 2022 ne a gasar. Lallai suna son Messi ya cigaba da kasancewa a ciki.”
Da yake tsokaci akan al’amarin, Collina ya yi watsi da iƙirarin a matsayin mara tushe, yana mai gargaɗin hakan ka iya zama haɗari ga alƙalan wasa da iyalansu.
A cewarsa, ƙera zance a harkar ƙwallon ƙafa abu ne da aka saba gani, amma ba za su lamunci zarge-zarge mara asali ba a fannin.

Ya ƙara da cewa, babu wanda zai yi iƙirarin wani zai iya juya lamuran alƙalancin FIFA wajen cimma manufarsa ciki har da shugaban FIFA, Gianni Infantino.
Duk da zargin jami’an gasar da nufin barin Argentina da Lionel Messi a gasar, FIFA ta jaddada cikakken yardarta ga alƙalan wasa da tsarin bincike na VAR.
