
Shugaba Bola Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa ƙudirin dokar gyaran Hukumar Kula da Manyan Makarantun Sakandare ta Ƙasa (NSSEC) na shekarar 2026, inda ya nemi da ta gaggauta amincewa da shi domin inganta tsarin gudanarwa da kula da manyan makarantun sakandaren gwamnati a Nijeriya.
Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ne ya karanta wasiƙar a zauren majalisar, ranar Alhamis.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa, Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da ƙudirin tun a taronta na ranar 30 ga watan Afrilu, 2026, kafin Ma’aikatar Shari’a ta tantance tare da kammala shirya shi bisa tanadin doka.
Shugaban ƙasar ya ce gyaran dokar na daga cikin manufofin gwamnatinsa na ƙarfafa cibiyoyin ilimi da inganta yadda ake tafiyar da harkokinsu a ƙasar.
Haka kuma, ya buƙaci Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta yi nazari tare da amincewa da kudirin cikin gaggawa domin inganta shugabanci da gudanar da manyan makarantun sakandare a faɗin ƙasar.
Ana ganin wannan ƙudiri a matsayin wani ɓangare na sauye-sauyen da gwamnatin tarayya ke son yi a tsarin ilimin sakandare a sassan ƙasar.
