Ministan muhalli ya yaba da ƙoƙarin Kano kan sauyin yanayi da farfaɗo da muhalli

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Ministan muhalli, Alhaji Balarabe Abbas Lawal, ya yabawa gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf kan irin ƙoƙarin da take yi wajen dashen bishiyoyi da farfaɗo da muhalli. Ya ce Kano ta zama abin koyi a Najeriya wajen aiwatar da matakan da ke taimakawa yaƙi da illolin sauyin yanayi.

Haka kuma ya sake tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da mara wa jihar baya wajen dawo da korayen filaye da bunƙasa muhalli.

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin bikin Ranar Babbar Katangar Kore ta 2026 (Great Green Wall Day), inda aka miƙa ofishin Hukumar Babbar Katangar kore ta ƙasa (NAGGW), aka kuma ƙaddamar da gangamin dashen bishiyoyi na 2026 da kuma rantsar da kwamitin jagoranci na ƙasa na aikin Scaling-Up Resilience in Africa’s Great Green Wall (SURAGGWA). Ya kuma nuna gamsuwarsa da yadda ayyukan kare muhalli ke gudana bayan duba wuraren da ake aiwatar da su a cikin birnin Kano.

Da yake jawabi a wajen taron, kwamishinan albarkatun ruwa, Muhalli da sauyin yanayi na Jihar Kano, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya bayyana cewa mayar da hedikwatar hukumar babbar Katangar Kore ta ƙasa zuwa Kano a matsayin wani babban cigaba ga manufofin kare muhalli da yaƙi da sauyin yanayi a Najeriya.

Ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da mayar da hedikwatar zuwa Kano, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta samar da duk wani yanayi mai kyau domin hukumar ta gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

Dakta Hashim ya ce wannan mataki zai ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da Jihar Kano wajen dawo da ƙasashen da suka lalace, yaƙi da yaɗuwar hamada da kuma inganta rayuwar al’ummomin Arewacin Najeriya. Ya kuma yabawa hukumar babbar katangar kore ta ƙasa kan gudummawar da take bayarwa ta hanyar dashen bishiyoyi, noma mai dacewa da sauyin yanayi, inganta amfani da ƙasa da kuma tallafa wa mata, matasa da gidaje masu ƙaramin ƙarfi.

Ya ƙara da cewa tallafin shukokin dabino 500,000 da hukumar ta bai wa Kano wata muhimmiyar gudummawa ce da za ta taimaka wajen bunƙasa samar da abinci, ƙara ayyukan yi da kuma ƙarfafa juriyar al’umma wajen fuskantar sauyin yanayi.

Game da nasarorin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf kuwa, Dakta Hashim ya ce Kano ta amince da manufofin sauyin yanayi, ta kammala tsarin aiwatar da manufofin, sannan ta ci gaba da aikin dokar sauyin yanayi ta Jihar Kano. Ya ce hakan ya taimaka wajen ɗaga matsayin Kano a ƙimar shugabanci kan sauyin yanayi daga matsayi na 34 a shekarar 2024 zuwa matsayi na huɗu a shekarar 2025.

Ya bayyana cewa jihar ta dasa shukokin bishiyoyi miliyan uku a shekarar 2024, yayin da a shekarar 2025 ta samar da shukoki miliyan 5.5, inda aka dasa sama da bishiyoyi miliyan biyar a makarantu, cibiyoyin gwamnati, al’ummomi da sauran muhimman wurare. Haka kuma an farfaɗo da fiye da hekta 50,000 na ƙasashen da suka lalace ta hanyar ayyukan hana zaizayar ƙasa, dashen bishiyoyi, samar da katangar bishiyoyi da sauran shirye-shiryen gyaran muhalli.

A ƙarshe, Dakta Hashim ya bayyana aikin SURAGGWA a matsayin wata muhimmiyar dama da za ta ƙara faɗaɗa ayyukan farfaɗo da muhalli, daidaitawa da sauyin yanayi da inganta hanyoyin samun abin dogaro ga al’umma. Ya kuma tabbatar wa gwamnatin tarayya, hukumar babbar katangar kore ta ƙasa, hukumar FAO, asusun GEF da sauran abokan hulɗar ci gaba cewa Jihar Kano a shirye take wajen tabbatar da nasarar aiwatar da aikin da kuma ci gaba da zama abin koyi a fannin kare muhalli a Najeriya.

By ukarofi