Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Bankin Jaiz, wanda shi ne bankin farko mai gudanar da harkokin kuɗi ba tare da ruwa ba a Nijeriya, na fuskantar warin matsin lamba daga ɓangaren shari’a da masu sa ido kan harkokin bankuna, bayan zargin cewa ya ƙi aiwatar da umarnin da Babbar Kotun Jihar Kano ta bayar na biyan kuɗin da kotu ta yanke.
Lamarin ya samo asali ne daga umarnin aarshe na kwace kuɗi domin biyan bashin hukunci (Garnishee Order Absolute) da kotun ta bayar a ranar 8 ga Janairu, 2026, a shari’ar da ke tsakanin Yahaya Usman a matsayin wanda kotu ta tabbatar za a biya haƙƙinsa da kuma Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a a matsayin wanda ake binsa.
A cewar rahotanni, kotun ta umarci Jaiz Bank ya fitar da kuɗaɗen da ke cikin asusun wanda ake binsa tare da miƙa su ga lauyoyin Yahaya Usman, wato Bright Attorneys.
Sai dai lauyoyin wanda ya ci shari’ar sun zargi bankin da gangan da ƙin bin umarnin kotu, tare da cewa ya yi amfani da dabarun jinkirta aiwatar da hukuncin domin bai wa wanda ake binsa damar ci gaba da shigar da buƙatu marasa tushe a gaban kotu.
A cikin wasiƙar da suka aikewa reshen bankin Jaiz da ke Titin Tafawa Balewa a Kano, lauyan Yahaya Usman, Usman Umar Fari, ya ce bankin ya taka rawa wajen kawo cikas ga aiwatar da hukuncin.
Lauyoyin sun kuma yi zargin cewa tun farko bankin ya gabatar da rantsuwar shaida yana iƙirarin cewa ba ya riƙe da wata kadara ko kuɗin wanda ake binsa, amma daga baya kotu ta gano hakan ba gaskiya ba ne kafin ta bayar da umarnin ƙarshe na biyan kuɗin.
Sun bayyana cewa duk hujjojin da bankin ke jingina da su wajen ƙin biyan kuɗin sun rushe, domin kotu ta yi watsi da dukkan buƙatun da wanda ake binsa ya shigar.
A cewarsu, kotu ta yi fatali da buƙatar soke hukuncin tare da ci tarar wanda ake binsa Naira 200,000, sannan a ranar 26 ga Yuni, 2026 ta sake yin watsi da buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin, inda ta ƙara ci shi tarar Naira 50,000.
Bayan wa’adin sa’o’i 48 da lauyoyin suka bai wa bankin Jaiz ya cika ba tare da bankin ya aiwatar da umarnin kotu ba, Bright Attorneys ta fara shirin neman a hukunta shugabannin bankin bisa zargin raina kotu.
A ranar 3 ga Yuli, 2026, kamfanin lauyoyin ya nemi Magatakardar Babbar Kotu ta 17 da ke Kano ta fitar da Form 48, wadda ke zama sanarwar hukuncin da ke jiran duk wanda ya ƙi bin umarnin kotu.
Baya ga hakan, lauyoyin sun ce za su kai ƙorafi ga hukumomin tsaro da masu sa ido kan harkokin bankuna, suna zargin wasu jami’an bankin da yin rantsuwar ƙarya da kuma kawo cikas ga gudanar da adalci.
Sun kuma bayyana cewa za su shigar da ƙorafi gaban Babban Bankin Nijeriya (CBN) da kuma Kwamitin Bankunan Nijeriya domin neman a ɗauki matakin ladabtarwa kan bankin Jaiz, bisa abin da suka kira halayen da suka saɓa wa ƙa’idodin aikin banki kuma ka iya lalata martabar tsarin shari’a.
Lauyoyin sun ce sun riga sun aika kwafen takardun neman hukuncin raina kotu zuwa sashen shari’a na hedikwatar Jaiz Bank da kuma ofishin magatakardar kotun.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, bankin Jaiz ko lauyoyinsa ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan zarge-zargen ko kuma matakin neman hukuncin raina kotun da aka fara kansu.
