Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya ƙaddamar da Kwamitin Aiki na Shugaban ƙasa kan Dokar Tsarin Aikin ’Yan Sanda ta ƙasa (National Policing Bill), domin tsara dokar da za ta ba da damar aiwatar da tsarin ’yan sandan jihohi a faɗin Nijeriya.
Shugaban Ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila, ne ya wakilce shi wajen ƙaddamar da kwamitin a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja.
ƙaddamar da kwamitin na zuwa ne bayan Majalisar Tarayya ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki na shekarar 2026 da ya tanadi kafa tsarin ’yan sanda biyu, wato ’Yan Sandan Tarayya da kuma ’Yan Sandan Jihohi 36.
Shugaba Tinubu ya ce duk da cewa gyaran kundin tsarin mulkin ya kafa tubalin wannan tsari, har yanzu ana buƙatar wata cikakkiyar doka da za ta fayyace yadda za a aiwatar da shi a aikace.
A cewarsa, dokar za ta ƙunshi tanade-tanade kan mafi ƙarancin ƙa’idojin aikin ’yan sanda, tantance shirin kowace jiha kafin kafa rundunarta, haɗin gwiwar gwamnatin tarayya da jihohi, tabbatar da bin haƙƙin ɗan Adam, ɗaukar nauyin kuɗaɗe da kuma hanyoyin tabbatar da gaskiya da riƙon amana. Ya ce manufar kwamitin ita ce samar da cikakkiyar daftarin dokar da za a miƙa wa Majalisar Tarayya ba tare da ɓata lokaci ba.
Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF), Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun, ya tabbatar da cewa gwamnoni za su mara wa shirin baya tare da hanzarta amincewa da gyaran kundin tsarin mulkin a majalisun dokokin jihohinsu. Ya ce tsarin ’yan sandan jihohi zai amsa buƙatar da ’yan Nijeriya suka daɗe suna yi ta samar da tsaro mai kusanci da al’umma, yana mai ƙara da cewa idan kowace jiha ta ɗauki kimanin jami’ai 6,000, za a samu kusan karin jami’an tsaro 200,000 a faɗin ƙasar.
Shi ma Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi, ya bayyana shirin a matsayin mataki mai muhimmanci duba da ƙalubalen tsaron da ƙasar ke fuskanta, inda ya buƙaci gwamnoni su tabbatar da amincewa da gyaran kundin tsarin mulki cikin gaggawa. A nasa ɓangaren, Shugaban ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA), Afam Osigwe, ya bayyana goyon bayan ƙungiyarsa ga kafa ’yan sandan jihohi, tare da jaddada buƙatar samar da ingantattun tanade-tanaden doka da za su hana amfani da rundunar wajen tauye haƙƙin jama’a ko cin zarafi.
