Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Majalisar Zartarwa ta Jihar Kaduna ta amince da sayen tan 6,000 na takiin zamani, kwatankwacin buhu dubu 120,000, domin rabawa ƙananan manoma a jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Ahmed Maiyaki, ya ce an ɗauki wannan mataki ne a taron majalisar da Gwamna Uba Sani ya jagoranta ranar Talata, a wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnati na ƙarfafa noma da bunƙasa samar da abinci.
Ya tunatar da cewa a watan Agustan 2025, gwamnatin jihar ta raba manyan motocin taki 400 kyauta ga manoma 100,000, sannan a shekarar 2024 ta aiwatar da mafi girman shirin rabon taki a tarihin jihar.
Majalisar ta kuma amince da mataki na biyu na gina hanyoyi guda 11 a ƙananan hukumomin Zariya da Sabon Gari domin inganta sufuri da bunƙasa tattalin arziki.
Haka kuma, an amince da Manufofin Koyar da ƙwarewar Rayuwa da kuma Manufofin Daidaito Tsakanin Mata da Maza a Fannin Ilimi, domin inganta ilimi, rage barin makaranta da kuma ƙarfafa matasa wajen samun aiki da dogaro da kai.
