Za mu aiwatar da ayyukan raya ƙasa kamar na Abuja a dukkan jihohin Nijeriya – Tinubu 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa za ta faɗaɗa irin ci gaban ababen more rayuwa da ake samu a Babban Birnin Tarayya (FCT) zuwa sassan Nijeriya.

Tinubu ya bayyana hakan ne a Abuja yayin ƙaddamar da sabuwar hanyar Transitway N2 da ta haɗa Babban Yankin Kasuwanci da Wuse, tare da gadoji biyu da hukumar babban birnin tarayya (FCTA) ta gina. Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya wakilce shi.

Ya ce gwamnati za ta tabbatar da cewa dukkan yankunan ƙasar sun amfana da hanyoyi, gadoji, layukan dogo da sauran muhimman ayyukan more rayuwa domin bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.

Tinubu ya yabawa ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, kan yadda yake jagorantar sauya fasalin Abuja bisa babban tsarin birnin.

A nasa jawabin, Wike ya ce saurin aiwatar da ayyukan raya ƙasa a FCT ya samu ne sakamakon goyon bayan Tinubu, musamman cire FCTA daga tsarin Treasury Single Account (TSA).

Ya kuma yi alƙawarin cewa za a sanya sabbin hanyoyin Abuja da ba su cikin Google Maps domin sauƙaƙa zirga-zirga.

By ukarofi

Leave a Reply