Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Majalisar Dattawa ta yanke shawarar jiran sakamakon binciken da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) ke gudanarwa kafin ɗaukar wani ƙarin mataki kan takaddamar da ta shafi abin da ake kira Majalisar Bunƙasa Shigar da Jari daga ƙasashen Waje ta Fadar Shugaban ƙasa (PFIPC) da kuma yadda aka saka ta cikin kasafin kuɗin shekarar 2026.
Matsayar ta biyo bayan wani ƙuduri da Sanata Suleiman Abdulrahman Kawu mai wakiltar Kano ta Kudu ya gabatar, inda ya buƙaci a gudanar da bincike cikin gaggawa kan kuɗaɗen da aka ware wa hukumar, ayyukanta da kuma yadda aka sanya ta cikin kasafin kuɗin ƙasa duk da zargin cewa ba ta da wata doka ko sahihancin kafa ta.
Da yake gabatar da ƙudurin a zaman majalisar, Sanata Kawu ya bayyana lamarin a matsayin babban abin damuwa ga cibiyoyin gwamnati, yana mai cewa takaddamar na iya jefa mutuncin Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya baki ɗaya cikin ƙalubale tare da rage amincewar jama’a ga tsarin kasafin kuɗin ƙasa.
Ya nuna cewa duk da bayanan da manyan jami’an Fadar Shugaban ƙasa suka fitar suna cewa PFIPC hukuma ce ta bogi wadda ba ta da wata sahihiyar kafa, an sanya ta cikin kasafin kuɗin shekarar 2026 ƙarƙashin lambar kasafi 0111062001, tare da ware mata jimillar kuɗi har Naira biliyan 1.302.
A cewarsa, cikin kuɗaɗen da aka ware akwai Naira miliyan 802.98 domin albashin ma’aikata, Naira miliyan 200 domin kuɗaɗen gudanarwa, da kuma Naira miliyan 300 domin ayyukan raya ƙasa.
Sanatan ya ce wannan ya haifar da tambayoyi masu yawa kan sahihancin tsarin shirya kasafin kuɗi da kuma yadda aka amince da shi.
Ya kuma buƙaci majalisar da ta yi Allah-wadai da duk wani gazawar gudanarwa, haɗin baki daga cikin gida ko kuma yiwuwar zamba da ta sa aka samu damar saka wata hukuma da ake zargin ba ta wanzu ba cikin kasafin kuɗin ƙasa.
Sai dai, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya ba da shawarar cewa a dakata da gudanar da binciken majalisa a halin yanzu, yana mai nuni da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya riga ya umarci ICPC da ta gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Barau ya ce: “Fadar Shugaban ƙasa ta riga ta ɗauki mataki ta hanyar umartar ICPC da ta binciki yadda wannan lamari ya faru. An riga an ba da umarni kuma ina ganin binciken ya fara.”
Ya ƙara da cewa: “A ganina, abin da ya dace mu yi yanzu shi ne mu jira rahoton ICPC, sannan daga baya mu ɗauki matakin da ya dace bisa sakamakon binciken.”
Bayan muhawarar da aka yi, Majalisar Dattawan ta amince da shawarar jiran rahoton ICPC kafin ɗaukar wani matakin majalisa kan lamarin PFIPC.
Wannan ci gaban na zuwa ne kwana guda bayan Shugaba Tinubu ya umarci ICPC da ta gudanar da cikakken bincike kan ayyukan PFIPC da duk wasu batutuwa da suka shafi hukumar, tare da gabatar masa da rahoto cikin kwanaki 30.
Tun da farko, Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa PFIPC ba hukuma ce da gwamnatin tarayya ta kafa ba, kuma ba ta da wata doka, amincewar shugaban ƙasa ko kuma hurumin gudanar da ayyuka a madadin gwamnati.
