Tsaro: Gwamnonin Arewa sun kafa asusun musamman na naira biliyan ɗaya duk wata 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnonin Arewa sun ƙaddamar da Kwamitin Amintattu na Asusun Tsaron Arewacin Nijeriya, tare da jaddada haɗin gwiwa da sarakunan gargajiya domin tinkarar matsalar tsaro.

Gwamnonin jihohin Arewacin Nijeriya sun ƙaddamar da Kwamitin Amintattu (Board of Trustees) na Northern Nigeria Security Trust Fund (NNSTF) tare da amincewa cewa kowace jiha za ta rika bayar da gudunmawar Naira biliyan ɗaya duk wata domin ƙarfafa ayyukan tsaro a yankin.

An cimma wannan matsaya ne a taron haɗin gwiwa na ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (Northern States Governors’ Forum) da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa, wanda aka gudanar a Sir Kashim Ibrahim House da ke Kaduna ranar Laraba.

 Blueprint Manhaja ta lura cewa taron ya tattaro gwamnoni, sarakunan gargajiya da manyan jami’an tsaro domin tattauna hanyoyin da za a magance matsalolin tsaro da ke ci gaba da addabar yankin Arewa.

Da yake jawabi bayan taron, Gwamnan Jihar Kaduna kuma mai masaukin baki, Uba Sani, ya ce tattaunawar ta kasance mai ma’ana, gaskiya da kuma mayar da hankali kan yadda za a samar da mafita mai ɗorewa ga matsalolin tsaro.

Ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro a Arewa ba za a iya shawo kanta ta hanyar kowace jiha ita kaɗai ba, yana mai cewa hakan na buƙatar haɗin kai tsakanin gwamnatocin jihohi, gwamnatin tarayya da kuma sarakunan gargajiya, waɗanda ke da kusanci da al’umma.

“Gina zaman lafiya mai ɗorewa na buƙatar haɗin gwiwa da kuma amfani da rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen sasanta al’umma da tattara bayanan sirri,” inji shi.

Babban abin da ya fito daga taron shi ne ƙaddamar da Kwamitin Amintattu na Northern Nigeria Security Trust Fund (NNSTF), wanda ya ƙunshi fitattun masana harkokin tsaro da dattawan Arewa.

Gwamnonin sun kuma sake tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da tallafa wa asusun ta hanyar bayar da Naira biliyan ɗaya duk wata daga kowace jiha mamba, domin samar da ingantaccen tsarin haɗin gwiwar tsaro a yankin.

Ana sa ran asusun zai taimaka wajen samar da kayan aiki, inganta musayar bayanan sirri da kuma tallafa wa shirye-shiryen haɗin gwiwa na hukumomin tsaro.

Har ila yau, gwamnonin sun sake bayyana goyon bayansu ga ƙoƙarin gwamnatin tarayya na inganta tsarin tsaro a ƙasar.

Sun yaba wa Bola Tinubu kan matakan da gwamnatin sa ke ɗauka wajen sake fasalin tsarin tsaron Nijeriya.

Taron ya kuma yi maraba da ci gaban da ake samu kan batun kafa Rundunar ‘Yan Sandan Jihohi (State Police), yana mai cewa lokaci ya yi da za a aiwatar da wannan gyara domin ƙarfafa tsaron al’umma.

A cewar gwamnonin, idan aka samar da ingantattun tanade-tanaden kundin tsarin mulki, ƙa’idojin aiki da tsarin sa ido, rundunar ‘yan sandan jihohi za ta ƙara inganta tsaron al’umma tare da kare rayuka da dukiyoyi.

Matsalar rashin tsaro ta dade tana addabar jihohin Arewa, inda hare-haren ‘yan bindiga, satar mutane, ta’addanci da rikice-rikicen manoma da makiyaya suka janyo asarar rayuka da dukiyoyi tare da shafar noma, kasuwanci da ilimi.

Masana harkokin tsaro sun sha bayyana cewa haɗin gwiwar jihohi da samar da isassun kuɗaɗen tallafa wa hukumomin tsaro na daga cikin muhimman hanyoyin da za su taimaka wajen rage matsalar.

Mazauna Kaduna sun yaba

Wasu mazauna Kaduna da suka zanta da Manhaja bayan taron sun yabawa gwamnatin jihar bisa karɓar baƙuncin taron da kuma matakin kafa asusun tsaron.

Malam Abdullahi Usman, wani ɗan kasuwa a Kaduna, ya ce: “Wannan mataki abin a yaba ne. Idan jihohin Arewa za su rika haɗa kuɗi domin tsaro, hakan zai taimaka wajen magance matsalolin da suka daɗe suna addabar yankin.”

Ita kuwa Hajiya Ladi Aboki, mazauniyar Unguwar Dosa, ta ce: “Mun yi farin ciki da yadda gwamnoni da sarakuna suka zauna wuri guda domin nemo mafita. Haɗin kai shi ne abin da Arewa ke buƙata a wannan lokaci.”

Shi ma Malam Yusuf Sani, wani malami mai ritaya, ya bayyana cewa: “Kafa Asusun Tsaron Arewacin Nijeriya babban ci gaba ne. Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kuma amfani da kuɗaɗen yadda ya kamata domin al’umma su ga sakamako.”

By ukarofi

Leave a Reply