Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Makarantar Madarasatul Irshadussibyan Islamiyya Lidarasatil Islamiyya Wa Tahfizul ƙur’an, da ke unguwar Darmanawa a ƙaramar Hukumar Tarauni ta jihar Kano, ta gudanar da walimar saukar Alƙur’ani ga ɗalibai 60.
Shugaban makarantar, Ustaz Mannir Bello, ya bayyana cewa ɗalibai 55 ne da kuma mata masu aure biyar suka kammala karatun Alƙur’ani a wannan karo na biyar da makarantar ta shirya irin wannan walima.
Taron ya samu halartar manyan baƙi daga sassa daban-daban na jihar Kano, inda aka kuma ƙaddamar da kalandar makarantar domin tallafa wa ayyukanta.
A wajen taron, AIG Ma’azu Yarima PhD, wanda shi ne shugaban taron, ya ƙaddamar da kalandar da naira dubu 200 tare da alƙawarin gina azuzuwa huɗu a makarantar.
Haka kuma, shugaban SGCPD, Dakta Yusuf Yau Gambo, ya sayi kalandar kan naira dubu 50 ta hannun wakilinsa.
Masu jawabi a wajen taron sun yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su tallafa wa cibiyoyin ilimi domin ci gaban al’umma.
