Kofin Duniya: An yi waje da baki ɗaya ƙasashen Afirka tara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Bajintar da Moroko ta riƙa nunawa a gasar Kofin Duniya na 2026 ya zo ƙarshe bayan shan kaye 2 da 0 a hannun Faransa a wasan kwata fainal, lamarin da ya kawo ƙarshen cigaba da fafatawa da ƙasashen Nahiyar Afirka a gasar.

Tawagar Atalsa Lions ta Moroko ce kaɗai ta samu damar kaiwa matakin daga cikin ƙasashen Afirka bayan ɗauki ba daɗi da ita daga tawagogin ƙasashe daban-daban na wasu nahiyoyi.

Ƙasashen Afirka guda tara ne suka samu kaiwa zagayen ‘yan 32 bayan kammala na rukunin-rukuni, inda a lokacin ne aka cire “DR Congo, South Africa, Ghana, Ivory Coast, Senegal, Cape Verde, da Algeria”.

Misra ma ta samu bin Moroko zuwa zagayen ‘yan 16, saidai ta samu cikas bayan da Argentina ta doke ta da ci 3 da 2.

By Babaji

Leave a Reply