Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kungiyar cigaban Funtua tayi kira ga Gwamna Dikko Raɗɗa, ‘yan majalisar ƙasa,Sarakuna, manyan ‘yan kasuwa da sauran masu faɗa a ji da su buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya bada umurnin gyaran honyoyin gwamnatin tarayya tun kafin damina ta tafi da wasu.
Shugaban ƙungiyar kwamred Mannir Suleiman wanda yayi wannan kira a Funtua a hira da manema labarai ya ce babu wata hanya ta gwamnatin tarayya a Katsina da bata lalace ba.
Kwamred Suleiman ya nuna rashin jin daɗin sa ga yadda gwamnatin tarayya ta zuba makudan kuɗi kan gyaran wasu hanyoyi a wasu ɓangaren ƙasa ba tare da la’akari da wasu jihohin Arewacin ƙasar musamman Jihar Katsina.
Ya ce hanyar Katsina zuwa Dutsinma ta miƙe zuwa mararrabar Ƙankara ta shafe shekara fiye da 30 ba gyaran wanda ya ƙara kawo taɓarɓarewar tsaro a hanyar.
Haka ma hanyar Kano zuwa Katsina wanda aka fara gina sabon hanyar amma da aka taso da aikin daga Kano “daidai iyakar Kano zuwa Katsina sai aikin ya tsaya ba tare da wani dalili ba.
“Haka ma hanyar Gidan Mutum Ɗaya zuwa Funtua yayi lalacewar da duk wani mai abin hawa yana fargabar bin hanyar,”Inji Suleiman.
Ya ce lalacewar honyoyin yasa ‘yan bindaga suke cin karan su ba babbaka musamman a hanyar Musawa zuwa Matazu da Dutsinma zuwa Ƙankara.
Shugaban ƙungiyar sai yayi Kira ga Gwamna Dikko Raɗɗa da ya jagoranci masu ruwa da tsaki a Jihar zuwa Abuja domin su gabatarwa shugaban ƙasa da wannan ƙorafi tun kafin damina ya katse wasu hanyoyi wucewa.
Shugaban ƙungiyar ya yabawa Gwamna Dikko Raɗɗa kan yadda ya gina manyan honyoyi da gyara wasu a manyan jihar.
Ya bada misali a yankin Funtua da gwamnan ya gina manyan tagwayen hanyoyi da gyara wasu a garin Funtua tare da sanya fitulu masu hasken rana domin kyautata tsaro da bunƙasa kasuwanci.
Kwamred Suleiman ya ce yanzu yankin Funtua za ta yi gogaiya da kowace birni a ƙasar nan ta ɓangaren ababen more rayuwa.
