Kin jinin baƙar fata: Majalisar Dattawa ta yi barazanar yanke hulɗar diflomasiyya da Afirka ta Kudu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Majalisar Dattawan Nijeriya ta yi gargaɗin cewa ƙasar za ta iya sake duba dangantakarta ta diflomasiyya da Afirka ta Kudu idan hare-haren ƙiyayya ga baƙi, musamman ‘yan Nijeriya, suka ci gaba a ƙasar.

Wannan matsaya ta biyo bayan wata sanarwa da Sanata Asuƙuo Ekpeyong ya gabatar a zauren majalisar, inda ya jawo hankalin sanatoci kan wa’adin da aka ce an bai wa ‘yan Nijeriya mazauna Afirka ta Kudu ranar 30 ga Yunin 2026, lamarin da ya bayyana a matsayin babbar barazana ga rayukansu da hanyoyin samun abincinsu.

Majalisar ta nuna damuwa kan yadda hare-haren ƙiyayya ga baƙi suka ci gaba da maimaituwa a Afirka ta Kudu, inda aka kashe wasu ‘yan Nijeriya tare da lalata dukiyoyinsu da kasuwancinsu a lokuta daban-daban, lamarin da ya janyo tsaiko a dangantakar ƙasashen biyu.

A yayin muhawarar, sanatoci sun buƙaci gwamnatin tarayya ta samu tabbataccen garanti daga gwamnatin Afirka ta Kudu kan kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya da ke zaune a ƙasar, tare da ɗaukar matakan diflomasiyya masu ƙarfi domin hana sake aukuwar irin waɗannan hare-hare.

Sanata Salihu Mustapha ya buƙaci gwamnatin tarayya ta ɗauki tsauraran matakai kan Afirka ta Kudu.

Ya ce, “Ba za mu ci gaba da zura ido ana kashe ‘yan Nijeriya tare da wawashe kasuwancinsu ba. Ina ganin ya kamata Nijeriya ta fara tunanin katse duk wata hulɗar diflomasiyya da Afirka ta Kudu.”

Sai dai tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Yahaya Abdullahi, ya buƙaci a yi taka-tsantsan, yana mai cewa akwai yiwuwar hare-haren na da alaƙa da wasu tsare-tsaren siyasa da ke neman kawo cikas ga gwamnatin Afirka ta Kudu.

Ya tunatar da irin rawar da Nijeriya ta taka a yaƙin kawo ƙarshen mulkin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu, da kuma goyon bayan da ta bai wa ƙungiyoyin ANC da SWAPO da FRELIMO.

A cewarsa, “Akwai wasu ƙoƙarin da ake yi na raunana gwamnatin Afirka ta Kudu da jam’iyyar ANC mai mulki. Saboda haka ya kamata mu yi taka-tsantsan kafin ɗaukar duk wani mataki.”

Sanatan ya kuma nuna damuwa kan ƙarancin kuɗaɗen da ake ware wa ofisoshin jakadancin Nijeriya a ƙasashen waje, yana mai cewa hakan na rage ƙarfin ƙasar wajen kare muradun ‘yan Nijeriya da ke zaune a ƙetare.

Bayan doguwar muhawara, Majalisar Dattawan ta amince da wasu kudurori da suka haɗa da umurtar Ma’aikatar Harkokin Waje da Babban Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Afirka ta Kudu su nemi rubutaccen tabbaci daga gwamnatin ƙasar kan tsaron ‘yan Nijeriya tare da neman kamo da hukunta waɗanda suka aikata hare-haren.

Haka kuma, majalisar ta buƙaci Hukumar ‘Yan Nijeriya Mazauna ƙasashen Waje (NiDCOM) da ofisoshin jakadanci su tattara bayanan duk ‘yan Nijeriya da suka rasa rayukansu ko suka jikkata ko aka lalata dukiyoyinsu domin neman diyya ta hanyar doka.

Majalisar ta kuma buƙaci gwamnatin tarayya ta yi aiki tare da Tarayyar Afirka da sauran ƙasashen da abin ya shafa domin samar da tsarin gargaɗin wuri da ɗaukar alhaki don dakile irin waɗannan hare-hare a nan gaba.

A yayin zaman, Sanata Abdul Ningi ya ba da shawarar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara shirye-shiryen katse hulɗar diflomasiyya da Afirka ta Kudu idan hare-haren suka ci gaba.

Shi ma Sanata Adams Oshiomhole ya ba da shawarar a riƙa amfani da ribar kamfanonin Afirka ta Kudu da ke aiki a Nijeriya wajen tallafa wa waɗanda hare-haren suka shafa.

Sai dai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, wanda ya jagoranci zaman, ya roƙi a dakata da waɗannan shawarwari har sai kwamitin majalisar ya kammala bincikensa.

Daga ƙarshe, an miƙa batun ga Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Waje domin gudanar da bincike tare da gabatar da rahotonsa cikin makonni biyu.

By ukarofi

Leave a Reply