
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Juma’a Jam’iyya mai mulki (APC) ta sanar a hukumance cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne abokin tafiyar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, tana mai bayyana ƙwarin-gwiwar samun gagarumar nasara.
APC ta tabbatar da haka ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce ta karɓi fom ɗinsu na tsaya wa takarar shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen da ke cigaba da kusantowa.
Shugaban jam’iyyar na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ne ya karɓi takardun da aka cike wa shugabannin a wani taro da aka gudanar a Abuja, inda mai ba shugaban ƙasa shawara skan harkokin siyasa, Ibrahim Masari ya miƙa takardun a madadin Shugaba Tinubu.
APC ta bayyana cewa, a yanzu za a miƙa takardun takarar zuwa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) domin kammala sauran matakan rajistar takara akansu.
A baya dai an yi ta yaɗa raɗe-raɗin cewa ta yiwu Tinubu ya ajiye Shettima ya ɗauki wani mutum daban daga arewa saboda cece-kucen da ake yi game da tikitin takarar Musulmi da Musulmi da wasu ke ganin tauye wani ɓangare ne a ƙasar mai mabanbanta addinai.

