Majalisar Wakilai ce ta saka ayyukan titina a kasafin kuɗin Hukumar Almajirai — NCAOOSCE

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Hukumar Kula da Ilimin Almajirai da Yara Marasa Zuwa Makaranta ta ƙasa (NCAOOSCE) ta bayyana cewa ayyukan gina titina da wasu ayyuka da suka bayyana a cikin kasafin kuɗinta na shekarar 2026 ba daga cikin ainihin ayyukan da aka kafa hukumar domin gudanarwa ba ne, illa ayyukan maza u da Majalisar Tarayya ta ɗora mata alhakin aiwatarwa.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai ba Babban Sakataren Hukumar shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Malam Nura Muhammad, ya fitar a ranar Talata a Abuja.

Tun da farko, Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa hukumar ta ware kimanin naira biliyan 8.4 domin ayyukan gina tituna a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026, lamarin da ya haifar da tambayoyi kasancewar aikin hukumar shi ne kula da ilimin almajirai da yara marasa zuwa makaranta.

Bayanan kasafin kuɗin shekarar 2026 sun nuna cewa an ware wa hukumar jimillar naira biliyan 22.82, wanda ya haɗa da naira biliyan 21.68 domin ayyukan raya ƙasa da kuma naira biliyan 1.14 domin gudanarwa.

Baya ga ayyukan tituna, kasafin kuɗin ya kuma ƙunshi sayen motocin asibiti, kayan aikin lafiya da kuma samar da wutar lantarki ta hasken rana.

Sai dai Nura Muhammad ya ce shigar da waɗannan ayyuka cikin kasafin kuɗin ya yi daidai da tsarin da aka saba amfani da shi, inda ake ɗora wa ma’aikatu da hukumomin gwamnati alhakin aiwatar da ayyukan mazabu da ‘yan majalisa suka gabatar.

Ya ce dukkan ayyukan da aka ɗora wa hukumar nauyin aiwatarwa za a gudanar da su ne bisa dokokin ƙasa da ƙa’idojin kashe kuɗaɗen gwamnati da kuma tsarin saye da bayar da kwangila.

A cewarsa, hakan ba ya nufin an sauya aikin da aka kafa hukumar domin yi, domin har yanzu babban aikinta shi ne inganta tsarin ilimin almajirai da rage yawan yara marasa zuwa makaranta a faɗin ƙasar nan.

Hukumar ta kuma bayyana cewa ta riga ta gano tare da tattara bayanan sama da yara 700,000 marasa zuwa makaranta a Nijeriya, tare da kafa cibiyoyin koyarwa guda 119 a sassa daban-daban na ƙasar.

Ta ƙara da cewa tana ci gaba da gudanar da wayar da kai daga unguwa zuwa unguwa tare da aiwatar da manufofin gwamnatin tarayya na sake fasalin tsarin almajiranci da magance matsalolin da ke tattare da shi.

Hukumar ta jaddada cewa kula da makomar almajirai da yara marasa zuwa makaranta shi ne babban abin da ta sa a gaba, tare da gode wa Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, da Karamin Ministan Ilimi, Farfesa Suwaiba Ahmad, bisa goyon bayan da suke ba ta wajen gudanar da ayyukanta.

By ukarofi

Leave a Reply