Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin dakatar da aiwatar da sabbin ƙa’idoji da dokokin da suka shafi dandamalin intanet, masu samar da ayyukan yanar gizo da sauran batutuwan tattalin arzikin zamani, har sai an kammala cikakken nazari da haɗa manufofin ƙasa guda ɗaya a wannan fanni.
An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Ministan Sadarwa, ƙirƙire-ƙirƙire da Tattalin Arzikin Zamani, Bosun Tijani, ya fitar a ranar Talata bayan wata ganawa da shugabannin Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC), Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta ƙasa (NITDA) da kuma Hukumar Kare Bayanai ta Nijeriya (NDPC).
Ministan ya ce, an ɗauki wannan mataki ne domin ci gaba da amfani da tsarin dokokin da ake da su a halin yanzu, yayin da ake aiki kan samar da haɗaɗɗiyar manufar ƙasa da kuma tsarin gudanar da harkokin tattalin arzikin zamani. A cewarsa, saurin bunƙasar tattalin arzikin zamani a Nijeriya ya haifar da cakuɗewar ayyuka tsakanin hukumomin da ke kula da wannan fanni, lamarin da ya sa ake buƙatar ingantacciyar haɗin kai domin samar da tabbas a doka, jawo hannun jari, ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire da kuma ƙara amincewar masu amfani da fasahar zamani.
Saboda haka, Gwamnatin Tarayya ta umarci hukumomin da abin ya shafa da su dakatar da aiwatarwa ko tilasta bin duk wata sabuwar doka, ƙa’ida, jagora, tsari ko umarni da aka fitar kwanan nan kan harkokin dandamalin intanet, masu shiga tsakani na yanar gizo da sauran batutuwan tattalin arzikin zamani da ke ƙarƙashin aikin daidaita manufofi.
Tijani ya bayyana cewa dokokin da ake amfani da su a yanzu za su ci gaba da aiki har sai an kammala aikin haɗa manufofin ƙarƙashin jagorancin ma’aikatarsa. Ya ce, wannan umarni ba ya hana kowace hukuma ci gaba da gudanar da ayyukan da doka ta ba ta iko a kansu, muddin sun yi daidai da sabon tsarin manufofin da ma’aikatar ta shimfiɗa.
Ministan ya kuma sanar da kafa Kwamitin Fasaha na Haɗin Gwiwa, wanda zai ƙunshi wakilai daga NCC, NITDA da NDPC, ƙarƙashin Ofishin Ministan. A cewarsa, kwamitin zai jagoranci tattaunawar fasaha, ya yi shawarwari da masu ruwa da tsaki a masana’antu, ƙungiyoyin fararen hula da masana ilimi, tare da gabatar da shawarwarin da za su haifar da haɗaɗɗiyar manufar ƙasa da tsarin gudanar da tattalin arzikin zamani.
Tijani ya bayyana cewa sabon tsarin da ake shirin samarwa zai fayyace nauyin da ya rataya a wuyan kowace hukuma, ya kawar da maimaita ayyuka tsakanin hukumomi, ya rage ruɗanin bin ƙa’idoji, ya ƙarfafa amincewar masu zuba jari, ya bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire, tare da tabbatar da cewa tsarin dokokin Nijeriya ya dace da burin ƙasar na zama jagora a fannin tattalin arzikin zamani a nahiyar Afirka da kuma ɗaya daga cikin wuraren da suka fi jan hankalin masu zuba jarin fasahar zamani a duniya. Ya ƙara da cewa, manufar wannan aikin ita ce inganta haɗin kai tsakanin hukumomi, ba wai rage ikon da doka ta ba kowacce hukuma ba.
Ministan ya tabbatar da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin samar da manufofin da za su ƙarfafa amincewa da tsarin fasahar zamani, bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire da kuma ɗaga darajar Nijeriya a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙasashen duniya a fannin tattalin arzikin zamani.
