Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babban Mai Bincike na Musamman da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa domin gudanar da bincike kan harkokin Babban Bankin Nijeriya (CBN) a zamanin tsohon gwamna Godwin Emefiele, Jim Obazee, ya buƙaci a faɗaɗa binciken shari’ar da ake yi kan zargin karkatar da dala miliyan 6.2 daga asusun musayar kuɗaɗen ƙasashen waje na Gwamnatin Tarayya da ke hannun CBN.
Obazee ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da yake ba da shaida a gaban Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya Abuja a madadin Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC), a shari’ar da ake yi wa Godwin Emefiele kan tuhume-tuhume guda 20 da suka haɗa da haɗa baki wajen aikata laifi, amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba da kuma zamba.
Shaidan, wanda Rotimi Oyedepo, SAN, Daraktan Gurfanar da Masu Laifi na Tarayya ya jagoranta wajen gabatar da shaida, ya nuna rashin jin daɗinsa bayan an gabatar masa da wasu wasiƙu da ake zargin marigayi tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sanya wa hannu domin a saki dala miliyan 6.2. Haka kuma, an gabatar masa da wata wasiƙa daga ofishin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, wadda ta umarci tsohon gwamnan CBN ya saki kuɗin ga wani Jibril Abubakar, wanda aka bayyana a matsayin ma’aikacin ofishin SGF.
Obazee ya ƙara nuna fushinsa bayan an gabatar da wasu bayanai da kuma rubuce-rubucen da Boss Mustapha ya yi, inda ya musanta cewa shi ko marigayi Buhari sun san da wasiƙun da suka umarci a saki kuɗin. A cewarsa, Mustapha ya yi iƙirarin cewa an ƙirƙiri takardun ne ta hanyar yin jabun sa hannunsu tare da haɗin gwiwar wasu ma’aikatan CBN.
Mai binciken ya bayyana cewa abin takaici ne yadda gwamnati ta gurfanar da Emefiele shi kaɗai kan zargin damfarar da ya ce ta shafi mutane sama da goma.
Ya buƙaci kotun da Alƙali Hamza Muazu ke jagoranta ta tabbatar an gurfanar da Boss Mustapha tare da Emefiele, yana mai cewa bai kamata a ware wasu da ake zargin suna da hannu a lamarin ba.
Obazee ya kuma buƙaci a binciki tare da gurfanar da Manajan reshen CBN na Abuja, yana mai cewa an saki kuɗin ba tare da bin ƙa’idojin tantancewa ba. Ya ce dokar CBN ta tanadi cewa dole ne a fara ajiye kwatankwacin kuɗin a naira kafin a saki dala miliyan 6.2.
Baya ga Buhari, Boss Mustapha da Emefiele, Obazee ya nemi a kama tare da gurfanar da Jibril Abubakar, wanda ya karɓi kuɗin bisa wasiƙar da ake zargin ta fito daga ofishin SGF, da kuma Bashirudeen Maishanu, ma’aikacin CBN, wanda ya ce ya amsa cewa yana cikin waɗanda suka karkatar da kuɗin, sannan ya mayar da dala 856,500 ga kwamitin binciken.
A cewarsa, idan aka gurfanar da duk waɗanda ake zargi da hannu a lamarin, hakan zai zama darasi ga masu aikata irin waɗannan laifuka a gaba.
A lokacin tambayoyin da lauyan Emefiele, Mathew Burka, SAN, ya yi masa, Obazee ya tabbatar cewa bai karɓo ko sisi daga hannun Emefiele ba, kuma babu wata hujja da ke nuna cewa an tura masa kuɗi daga waɗanda ake zargi da aikata laifin.
Sai dai ya ce bisa fahimtarsa, Emefiele ya kamata ya san abin da ya faru idan har an yi amfani da tsarin kyamarorin sa ido (CCTV) da kuma tsarin tantance bayanan BVN a reshen CBN na Abuja kafin a saki kuɗin.
Obazee ya ƙara da cewa da an gudanar da binciken kuɗaɗen CBN yadda ya kamata a cikin rahoton kuɗaɗen shekara-shekara, da an gano bacewar kuɗin tun da wuri.
Ya kuma shaida wa kotu cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gayyace shi a ranar 19 ga Disamba, 2023, inda a gaban Lateef Fagbemi da shugaban EFCC, aka umarce shi da ya shirya tuhume-tuhumen da za a gurfanar da Emefiele a kansu dangane da zargin karkatar da dala miliyan 6.2.
Sai dai lokacin da aka tuna masa cewa an riga an shirya takardar tuhume-tuhumen tun ranar 14 ga Agusta, 2023, Obazee ya ce shi ba lauya ba ne, don haka ba zai iya yin bayani kan wannan batu ba.
Daga ƙarshe, Alƙali Hamza Muazu ya ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 20 ga Oktoba.
