Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani mummunan al’amari ya auku a ƙauyen Gongo da ke ƙarƙashin gundumar Limawa a ƙaramar hukumar Dutse ta Jihar Jigawa, inda tsawa ta kashe wani mutum mai shekara 30 tare da jikkata yara biyu, lamarin da ya sake tayar da hankalin mazauna yankunan karkara kan haɗarin tsawa da ke yawan faruwa a yankin.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:15 na yammacin ranar 22 ga Yunin 2026, lokacin da wata guguwar ruwan sama mai ƙarfi tare da tsawa da walƙiya ta afkawa ƙauyen, wanda ke da tazarar kusan kilomita biyar gabashin birnin Dutse.
Mamacin, Iliya Alhaji Sabo, mai shekara 30, ya rasu nan take bayan walƙiya ta same shi. Marigayin ya bar mata guda ɗaya da yara uku. Baya ga haka, yara biyu – Salim Murtala mai shekara tara da Hassan Adamu mai shekara biyar – sun samu raunuka sakamakon wannan tsawa.
ɗaya daga cikin waɗanda suka fara isa wurin, Malam Adamu Mu’azu, wanda aka fi sani da Adamu Dan Yaya, kuma ɗan uwan mamacin ne, ya ce yana cikin gidansa lokacin da ya ji ihun yara. Ya ce, da ya fito yayin da ruwan sama da tsawa ke ci gaba, sai ya tarar da Iliya kwance a ƙasa bayan tsawa ta same shi, yayin da yaran biyu su ma suka jikkata. Mu’azu ya ce nan take suka garzaya da waɗanda abin ya shafa zuwa Babban Asibitin Dutse, inda likitoci suka tabbatar da rasuwar Iliya bayan isarsu.
Sarkin ƙauyen Gongo, Malam Yusufu Alhaji Ali, ya bayyana cewa tsawa ta zama matsala da ke yawan addabar aauyen. Ya ce, kusan duk shekara ko bayan shekara biyu tsawa kan afka wa ƙauyen, kuma a wasu lokutan ma tana afkuwa sau biyu cikin shekara guda. A cewarsa, tsawa ta taɓa kashe wata babbar bishiyar ɗorawa da ke yammacin ƙauyen, sannan a gabashinsa ta lalata wata bishiyar dabino. Ya roƙi gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su kawo ɗauki kafin ƙarin rayuka su salwanta.
A ƙoƙarin gano hanyoyin rage mace-macen da tsawa ke haddasawa, wakilin Manhaja ya tattauna da Dr. Babagana Abubakar, mamba a Kwamitin Gudanarwa na Cibiyoyin Ilimantar da Jama’a Kan Tsawa na Afirka (African Centres for Lightning Education Network – ACLEnet). Ya bayyana cewa ƙungiyar na aiki ne domin rage mace-mace, raunuka da asarar dukiyoyi da tsawa ke haddasawa a faɗin nahiyar Afirka.
A cewarsa, suna cimma hakan ta hanyar inganta tsarin gargaɗin tsawa, wayar da kan jama’a kan hanyoyin kariya da kuma inganta ƙa’idojin gina na’urorin kariya daga tsawa. Ya shawarci jama’a da kada su nemi mafaka ƙarƙashin bishiyoyi yayin tsawa, su nisanci koguna, tafkuna, wuraren wanka da duk wasu abubuwan ƙarfe.
Idan mutum ya tsinci kansa a fili ba tare da mafaka ba, ya ce ya kamata ya tsugunna a kan tafin ƙafafunsa tare da haɗe ƙafafu da sunkuyar da kai, maimakon kwanciya a ƙasa.
Ya kuma gargaɗi jama’a da kada su yi amfani da famfo, shawa, wayoyin tarho masu igiya ko na’urorin lantarki da ke haɗe da wutar lantarki yayin tsawa.
Haka kuma ya ba da shawarar girka ingantattun na’urorin kariya daga tsawa da kuma na’urorin kare kayan lantarki daga bugun ƙarfin wuta.
Dr. Abubakar ya ce ACLEnet na taimaka wa al’ummomi ta hanyoyi huɗu, ciki har da girka na’urorin kariya daga tsawa a makarantu da cibiyoyin gwamnati cikin rahusa, gudanar da gangamin wayar da kai, horas da injiniyoyi da masu zanen gine-gine bisa ƙa’idojin ƙasa da ƙasa na kariya daga tsawa (IEC 62305), da kuma haɗin gwiwa da gwamnatocin Afirka wajen samar da manufofin kariya daga tsawa.
Mazauna yankin sun ce ba ƙauyen Gongo kaɗai ne ke fama da wannan matsala ba. A ƙauyen Galadanci, tsawa ta lalata injin niƙa mallakin wata mata, abin da ya hana ta hanyar samun kuɗin shiga. Haka kuma a ƙauyen Tagwaye, tsawa ta kashe dabbobi da dama a lokacin wata guguwa da ta afku a shekarar 2024.
Mazauna yankin sun ce yawaitar irin waɗannan al’amura na nuna muhimmancin ƙara wayar da kan jama’a, samar da ingantattun hanyoyin kariya daga tsawa da kuma sa hannun gwamnati domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
