Tinubu ya umarci a kula da lafiyar ɗalibai da malaman Oyo da aka ceto

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa game da nasarar ceto yara da malaman da aka yi garkuwa da su a ƙauyen Oriire da ke Ogbomoso a Jihar Oyo, yana mai yaba wa Rundunar sojoji, DSS da Rundunar ‘Yan sanda kan kawo ƙarshen kwanaki 57 da mutanen suka shafe a komar ‘yan bindiga.

Shugaban ya ce, atisayen jami’an tsaro ya yi sanadiyyar kama masu garkuwa guda takwas yayin da aka halaka wasu da dama, lamarin da ya sa mutanen suka shaƙi iskar ‘yanci da kuma sauƙi ga iyalansu da ƙasa baki ɗaya.

A sanarwar da Kakakinsa Bayo Onanuga ya fitar a ranar Juma’a, Tinubu ya jinina wa hukumomin tsaro bisa abin da ya kira da “aiki tuƙuru wajen ceto ‘yan makarantar”.

Ya kuma tausaya wa ‘yaran, malaman da kuma iyalan nasu akan halin ƙuncin da suka tsinci kansu a ciki na tsawon lokacin da suka ɗauka a tsare.

Haka kuma, ya yaba wa gwamnatin jihar Oyo bisa haɗin kan da ta bayar a ayyukan ceto mutanen, inda ya yi kira ga jihar da ta ƙarfafa tsaro a makarantu domin kauce wa sake faruwar irin haka a nan gaba.

Kazalika, shugaban ya umarci hukumomin bayar da agajin gaggawa da su yi aiki tare da gwamnatin jihar wajen ganin an samar wa yara da malaman kulawar magani da ta dace domin su samu dawowa cikin kuzarinsu.

By ukarofi

Leave a Reply