Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi watsi da buƙatar belin tsohon AGF na riƙo, Nwabuoku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja, ta yi watsi da buƙatar bayar da beli da tsohon muƙaddashin Akanta Janar na Ƙasa (AGF), Anamekwe Nwabuoku ya gabatar domin a sako shi daga gidan yari.

A ranar 23 ga Maris ne Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa Nwabuoku hukuncin ɗaurin shekaru 72 bayan samun sa da hannu a laifukan dq suka shafi halasta kuɗaɗen haram da almundahanar wasu maƙudan kuɗaɗe da adadinsu ya kai miliyan N868.4.

Mai shari’a James Omotosho ya bayyana cewa Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta gabatar da isassun hujjoji da suka tabbatar da laifukan da ake tuhumar Nwabuoku da su.

Akan haka ne kotun ta yi watsi da buƙatar bada belin nasa, wanda ke nufin zai cigaba da zaman gidan yarin bisa hukuncin da aka yanke masa a baya.

An tasa ƙeyar Nwabuoku ne a gidan yari bisa samun sa da aikata laifuka guda tara inda akan kowane guda daga ciki zai yi zaman kurkuku na shekara takwas, lamarin da ya sa adadin shekarun suka kai 72.

By Babaji

Leave a Reply