Har yanzu mutane 79 na hannun ‘yan ta’adda – Ndume ga sojoji bayan ceto ‘yan Oyo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanata Ali Ndume na Borno ta Kudu, ya yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen ceto mutanen mazaɓarsa da har yanzu suke hannun ‘yan ta’adda.

Ndume ya bayyana haka ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a.

Ya ce, duk da nasarar ceto ɗalibai da malamai da aka sace a Jihar Oyo daga ɓangaren dakarun tsaro, har yanzu akwai sama da mutane 42 da aka sace a mazaɓarsa, yayin da wasu fiye da 80 kuma ke cigaba da zama a hannun masu garkuwa da su.

Don haka ne ya buƙaci rundunar soji ta karkata hankalinta zuwa Borno ta Kudu domin ceto sauran mutanen da ke tsare, yana mai cewa iyalansu na cigaba da jiran dawowarsu gida cikin zullumi.

Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da ceto ɗalibai da malaman makarantar Jihar Oyo da aka sace, waɗanda suka shafe kwanaki 57 a hannun ‘yan ta’adda.

A yayin haka ne aka yi nasarar kama ‘yan bindiga takwas da halaka wasu da dama, lamarin da ya sa ‘yan makarantar yankin na Ogbomoso da ke jihar suka shaƙi iskar ‘yanci.

By ukarofi

Leave a Reply