Aminu Jaji ya yaba da sake tsayar da Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu na 2027

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD Gusau

Ɗan Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Dr. Aminu Sani Jaji, ya bayyana sake tsayar da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a matsayin babban ƙwarin gwiwa ga damar jam’iyyar All Progressives Congress APC a zaɓen.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis kuma Jamilu Iliyasu Birnin Magaji, mataimakin sa na yaɗa labarai ne ya sanya hannu, Jaji ya ce wannan shawara ta tabbatar da alƙiblar gwamnati kuma alama ce ta ci gaba ga APC gabanin babban zaɓen 2027.

Dr. Jaji, wanda ke wakiltar mazaɓar Ƙaura Namoda/Birnin Magaji ta tarayya a jihar Zamfara, ya ce sake zaɓar Shettima a matsayin abokin takara mataki ne mai muhimmanci zuwa ga nasarar jam’iyyar All Progressives Congress APC a babban zaɓen 2027 a ƙasar nan.

Ya ce sake tsayar da shi na nuna cewa Shugaba Tinubu yana da ƙwarin gwiwa kan yadda mataimakin shugaban ƙasan ya yi aiki cikin shekaru uku da suka gabata.

“Shawarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta nuna ƙwarin gwiwarsa kan goyon bayan da ba ya raguwa, aminci, ƙwazo, ƙwarewa da gudunmawa mai matuƙar muhimmanci da mataimakin shugaban ƙasa ya bayar ga gwamnati da ƙasa baki ɗaya,” in ji Jaji.

Ɗan majalisar ya ƙara da cewa wannan shi ne shawarar da ta fi hikima a yanzu.

Ya ce hakan ya ba jam’iyyar hanya bayyananne zuwa nasara a kowane mataki.

Jaji, wanda shi ne jagoran ƙungiyar siyasa ta Jajiya Movement a Nijeriya, ya ce ƙungiyar ta riga ta amince da tikitin Tinubu/Shettima na 2027.

A cewarsa, tikitin zai sake samun amincewa da ƙuri’un ‘yan Najeriya a zaɓen 2027.

Haka kuma, a madadinsa da na ƙungiyar Jajiya Political Movement, ya gode wa Shugaba Tinubu bisa ci gaba da riƙe Shettima a tikitin.

A sanarwar an buƙaci mataimakin shugaban ƙasa da ya ci gaba da jajircewa wajen cimma burin gwamnati.

“Na sake taya mai girma mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima GCON murnar haka, kuma ina addu’ar Allah maɗaukakin ya ba shi karin hikima, ƙarfi da lafiya domin ya ci gaba da yi wa ƙasa hidima tare da shugabanmu mai kishin ƙasa Bola Ahmed Tinubu wajen cigaba, kwanciyar hankali da wadata a Najeriya,” in ji Jaji.

By ukarofi

Leave a Reply