2027: Kiristocin Neja sun nemi a ba su kujerar mataimakin gwamna

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Kiristocin Jihar Neja ƙarƙashin inuwar Coalition of Concerned Christian Stakeholders sun bukaci Gwamna Mohammed Umaru Bago da ya zaɓi ɗan takarar Kirista a matsayin mataimakinsa a zaɓen gwamnan jihar na shekarar 2027.

ƙungiyar ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a Minna ranar Talata, inda ta ce an daɗe ana nuna wa Kiristoci wariya a harkokin mulki da shugabanci a jihar.

Ta ce, “Muna kira ga gwamna da shugabannin jam’iyyar APC da su tabbatar da fitowar ɗan takarar mataimakin gwamna daga cikin Kiristoci a zaɓen 2027. Muna ƙin amincewa da ci gaba da tsarin tikitin Musulmi da Musulmi duk da gudunmawar da muke bayarwa da kuma yawanmu a jihar.”

Da yake jawabi ga manema labarai, shugaban ƙungiyar, Honarabul Jonathan ɓatsa, ya ce Kiristoci sun kai sama da kashi 45 cikin 100 na al’ummar jihar, amma duk da haka an ci gaba da mayar da su baya a harkokin gwamnati.

Ya ce a zaɓukan fidda gwani na APC da suka gabata, wasu fitattun ‘yan siyasar Kirista da suka nuna sha’awar tsayawa takara an tilasta musu janye aniyarsu saboda addininsu.

ɓatsa ya bayyana cewa idan Kiristoci sun yi haƙuri da irin wannan yanayi a zaɓen 2023, ba za su sake amincewa da hakan a wa’adin mulki na biyu na Gwamna Bago ba.

Ya bayyana tsarin tikitin Musulmi da Musulmi a matsayin wanda bai dace da yanayin bambancin addinai da ke akwai a jihar ba, yana mai cewa akwai ƙwararrun ‘yan siyasar Kirista musamman daga yankin Sanatan Neja ta Gabas (Zone B) da suka cancanci kujerar mataimakin gwamna.

“Bayanan da muke da su sun nuna cewa mafi yawan Kiristocin jihar suna yankin Neja ta Gabas. Saboda haka, akwai buƙatar a yi adalci ta hanyar zaɓar mataimakin gwamna daga cikin Kiristoci,” inji shi.

Ya ƙara da cewa duk da cewa Kiristoci sun mara wa Gwamna Bago baya a zaɓen 2023, a wannan karon suna buƙatar tikitin APC ya nuna adalci, daidaito da haɗin kai ta hanyar bai wa Kirista damar zama mataimakin gwamna.

A cewarsa, bayan tattaunawa da shawarwari da dama, ƙungiyar ta amince da bai wa Gwamna Bago cikakken goyon baya a ƙoƙarinsa na neman wa’adi na biyu idan har ya amince da wannan buƙata ta su na zaɓar mataimakin gwamna daga cikin Kiristoci.

By ukarofi