Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shekaru uku bayan gwamnatin tarayya ta yi alƙawarin samar da asusun tallafi na Naira biliyan 200 domin rage tasirin sauye-sauyen tattalin arziki ga masana’antu da ƙananan ’yan kasuwa, masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa har yanzu yawancin waɗanda aka yi niyyar tallafawa ba su amfana da shirin ba.
A lokaci guda kuma, miliyoyin ƙananan kasuwanci sun durƙushe tare da rufe ƙofofinsu.
Kungiyar Masu ƙananan Kasuwanci ta Nijeriya (ASBON) ta ce kusan ƙananan kasuwanci miliyan biyu ne suka rufe tsakanin shekarun farko uku na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, sakamakon cire tallafin man fetur, sauye-sauyen tsarin canjin kuɗi, hauhawar farashi, tsadar gudanar da kasuwanci da kuma raguwar ƙarfin sayen jama’a.
Yayin da gwamnatin ke cika shekara uku a kan mulki, ƙungiyoyin ’yan kasuwa na ci gaba da neman bayani kan makomar shirin tallafin da aka sanar a shekarar 2023 domin taimaka wa kasuwanci su shawo kan matsalolin da sauye-sauyen tattalin arziki suka haifar.
A wani jawabi da ya yi wa ’yan Nijeriya a ranar 31 ga Yulin 2023, Shugaba Tinubu ya sanar da ware Naira biliyan 75 domin tallafa wa masana’antu, tare da ƙarin Naira biliyan 125 ga ƙananan da matsakaitan masana’antu da kasuwanci (MSMEs).
An tsara shirin ne domin samar da rance mai ƙarancin ruwa, inda masana’antu za su iya samun har zuwa Naira biliyan 1 da ruwa kashi tara cikin ɗari, yayin da ƙananan kasuwanci za su iya samun rancen har zuwa Naira miliyan 1.
Shugaban ƙasar ya bayyana a lokacin cewa za a fara raba kuɗaɗen ne tsakanin watan Yulin 2023 da Maris 2024. Sai dai shirin bai fara aiki a lokacin da aka tsara ba.
Sai a ranar 22 ga Afrilun 2024 ne tsohuwar Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Doris Uzoka-Anite, ta sanar da fara rabon tallafin.
Bayan fara shirin, wasu masu ruwa da tsaki sun lura cewa an rage kuɗin da aka ware wa ƙananan kasuwanci daga Naira biliyan 125 zuwa Naira biliyan 75, ba tare da wata cikakkiyar sanarwa daga gwamnati ba.
Shugaban ƙungiyar ASBON na ƙasa, Dakta Femi Egbesola, ya shaida cewa da dama daga cikin mambobinsu da suka nemi rancen har yanzu ba su samu wani tallafi ba.
A cewarsa, wasu sun samu tallafin ƙananan kasuwanci na Naira 50,000 da aka gabatar a ƙarƙashin shirin, amma manyan rancen da za su taimaka wajen bunƙasa kasuwanci da ceton su daga durƙushewa sun kasance abin da mafi yawan masu nema ba su samu ba.
“Wasu daga cikin mambobinmu sun samu tallafin Naira 50,000, amma a yanayin tattalin arzikin yau, wannan kuɗi ba zai wadatar wajen rage wa kasuwanci matsin lamba ba,” inji Egbesola.
Ya ƙara da cewa, tun daga shekarar 2024 ne masu neman rancen ke jiran a saki kuɗaɗen ba tare da sanin lokacin da hakan zai faru ba.
A cewar ASBON, jinkirin rabon tallafin ya rage tasirin da ake sa ran zai yi, domin da yawa daga cikin kasuwancin da aka yi niyyar tallafawa sun riga sun rufe.
ƙungiyar ta ce, kusan ƙananan kasuwanci miliyan biyu ne suka durƙushe tun bayan fara gwamnatin Tinubu.
Ta danganta hakan da tsadar makamashi, tashin gwauron zabi a farashin canjin kuɗi, hauhawar farashi, raguwar buƙatar kayayyaki da kuma wahalar samun rance mai sauƙi.
Masana sun yi gargaɗin cewa rufe irin wannan adadi mai yawa na kasuwanci zai yi mummunan tasiri ga samar da ayyukan yi, kuɗaɗen shiga na iyalai da ci gaban tattalin arzikin ƙasa, la’akari da muhimmiyar rawar da ƙananan kasuwanci ke takawa a Nijeriya.
Haka kuma, ƙungiyar Masana’antun Nijeriya (MAN) ta nuna damuwa kan ƙalubalen da masana’antu ke fuskanta, tana mai cewa samun rance mai sauƙi da ɗorewa na da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa harkokin masana’antu.
Babban Daraktan MAN, Segun Ajayi-Kadir, ya taɓa bayyana cewa ko da an saki dukkan Naira biliyan 200 ɗin, ba za su wadatar wajen magance matsalolin kuɗaɗen da masana’antu ke fuskanta ba.
Ya jaddada cewa abin da ake buƙata shi ne samar da hanyoyin samun rance mai sauƙin ruwa na dogon lokaci maimakon tallafin lokaci guda.
ƙungiyar ASBON ta kuma bukaci gwamnati da ta ɗauki matakan gyara yanayin gudanar da kasuwanci gaba ɗaya.
Egbesola ya ce rage kuɗin rajistar kasuwanci, samar da rangwamen haraji ga MSMEs da inganta wutar lantarki za su fi taimakawa kasuwanci fiye da shirye-shiryen tallafin wucin gadi.
A cewarsa, warware matsalolin tsarin tattalin arziki zai taimaka wajen rage tsadar gudanar da kasuwanci da kuma ƙara wa kamfanonin Nijeriya damar yin gogayya da takwarorinsu.
Ya yi gargaɗin cewa matuƙar ba a aiwatar da gyare-gyare masu ma’ana ba, kuɗaɗen tallafi kaɗai ba za su iya ceton ƙananan kasuwanci daga matsalolin da suke ciki ba.
Yayin da ’yan kasuwa da dama ke ci gaba da fama da matsin tattalin arziki, tallafin Naira biliyan 200 da gwamnatin tarayya ta yi alƙawari ya ci gaba da zama wani buri da har yanzu ba a cika ba a idanun masu anfani da shi
