Ƙungiyar Matasan Arewa ta sasanta ƙungiyoyin ’yan daba masu gaba da juna a Kano

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata ƙungiyar matasan Arewa ta Arewa Youth Merger Group (APC) ta samu nasarar sasanta ƙungiyoyin ’yan daba masu gaba da juna a Jihar Kano, a wani yunƙuri na rage rikice-rikicen tituna, satar wayoyin hannu, shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da kuma fashi da makami a sassan jihar.

Shirin sulhun ya samu goyon bayan hukumomin tsaro, ƙungiyoyin matasa, sarakunan gargajiya da kuma Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta hanyar manufofin Kano First Agenda.

A yayin taron sasancin, Mai Kula da ƙungiyar a Matakin Ƙasa, Hon. Musa Mujahid Zaitawa, ya ƙaddamar da rabon fom na rajista ga matasa marasa aikin yi da ke da alaƙa da harkokin daba da shaye-shaye.

Ya bayyana cewa za a miƙa sunayen waɗanda suka cike fom ɗin ga Gwamnatin Jihar Kano domin a ba su damar samun horon sana’o’i tare da tallafin jari, domin su dogara da halal wajen neman abin masarufi.

Zaitawa ya ce harkar daba na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa rashin tsaro a Kano, yana mai cewa bai wa matasa horon sana’a da tallafin tattalin arziki zai taimaka matuƙa wajen rage aikata laifuffuka.

Ya kuma yi kira ga fitattun attajiran Arewa da suka haɗa da Aliko Dangote, Abdussamad Isyaku Rabiu, A.A. Rano, A.Y. Maikifi, Bashir Dankullu, Sabiu Bako, Bureza, Danlami Alasan, Hamisu Dankaka da Yahaya Lawan, tare da kamfanonin Mudassir and Brothers da Garba Karfe Investment, da su haɗa hannu da ƙungiyar wajen tallafa wa shirin gyaran rayuwar matasan da abin ya shafa.

Haka kuma ya buƙaci iyaye su ƙara sanya ido kan tarbiyyar ’ya’yansu domin daƙile yaɗuwar shaye-shaye da sauran ayyukan ta’addanci.

Zaitawa ya gargaɗi ’yan siyasa da su guji amfani da matasa wajen tayar da tarzoma a lokacin yaƙin neman zaɓen shekarar 2027. Ya kuma roƙi hukumomin tsaro da su tabbatar da cewa duk matashin da aka sasanta amma ya koma aikata laifi, ya fuskanci hukuncin doka ba tare da sassauci ba.

Ya kuma yi kira ga Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II, da ya umarci hakimai, masu unguwanni da shugabannin ƙauyuka su riƙa sanya ido kan baƙin da ke shigowa jihar, domin ƙarfafa tsaron al’umma.

A cewarsa, sasanta ƙungiyoyin ’yan daban ba wai kawai zai kawo ƙarshen rikice-rikice da laifukan titi ba ne, har ma zai hana matasa masu raunin zuciya faɗawa hannun ƙungiyoyin ta’addanci.

Har ila yau, ya roƙi Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, da Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, da su tura ƙarin jami’an tsaro zuwa Kano domin hana ’yan bindiga kutsowa daga Jihar Katsina.

Duk da cewa ya bayyana Kano a matsayin ɗaya daga cikin jihohin da suka fi kwanciyar hankali a yankin Arewa maso Yamma, Zaitawa ya yi gargaɗin cewa sabbin barazanar tsaro na iya ƙaruwa yayin da harkokin siyasar zaɓen 2027 ke ƙara ƙamari.

Ya bayyana fatan cewa za a faɗaɗa shirin sasanci da wayar da kai zuwa faɗin jihar domin ilmantar da matasa kan illolin daba da shaye-shaye, tare da bunƙasa zaman lafiya mai ɗorewa.

By ukarofi

Leave a Reply