Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta sanar da kama wata tsohuwa mai shekaru 67 mai zama ’yar Nijeriya da Birtaniya, bayan jami’anta sun gano kilogiram 13 na hodar iblis da aka ɓoye cikin ɓawon ayaba na jabu, aka haɗa su da kayan abinci a cikin jakarta a Filin Jirgin Sama na ƙasa da ƙasa na Murtala Muhammed da ke Legas.
A cewar hukumar, wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, an kama wacce ake zargin, mai aikin kula da tsofaffi a Birtaniya, a harabar tashi ta Terminal 2, yayin da take ƙoƙarin shiga jirgin ɓirgin Atlantic zuwa birnin London a ranar 28 ga Yunin 2026.
Binciken da jami’an NDLEA suka gudanar kan jakarta ya kai ga gano manyan kunshi 31 na hodar iblis, waɗanda aka shirya cikin fasaha domin su yi kama da gungun ayaba. Jimillar nauyinsu ya kai kilogiram 13.
Rahoton ya ce yayin gudanar da bincike, matar ta amsa cewa haramtattun kayan nata ne.
