Ghana ta ɗage taron haɗin gwiwa da Afirka ta Kudu saboda hare-haren ƙyamar baƙi

Spread the love

Gwamnatocin Ghana da Afirka ta Kudu sun ce dangantakarsu na nan daram duk da jinkirta taron haɗin gwiwa. Gwamnatin ƙasar Ghana ta sanar da ɗage taron haɗin gwiwa da aka shirya gudanarwa da Afirka ta Kudu a watan Agusta, saboda yadda hare-haren da ake kai wa baƙin haure a ƙasar ta Afirka ta Kudu suka ƙara ƙamari a cikin ‘yan watannin nan.

Mai magana da yawun gwamnatin Ghana, Feliɗ Kwakye Ofosu, ya bayyana cewa idan aka gudanar da taron a halin da ake ciki yanzu, tabbas batun hare-haren ƙyamar baƙi ne zai mamaye tattaunawar, maimakon muhimman batutuwan haɗin gwiwar da ƙasashen biyu suka shirya tattaunawa a kansu.

Ya bayyana haka ne yayin wata hira da gidan rediyon Joy FM, inda ya ce ya fi dacewa a jira har sai yanayin ya lafa kafin shugabannin ƙasashen su sake zama domin tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban dangantakar ƙasashen biyu.

An shirya gudanar da taron ne a Ghana, inda ake sa ran Shugaban Ghana, John Dramani Mahama, da takwaransa na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, za su jagoranci zaman a ƙarƙashin Kwamitin Haɗin Gwiwa na ƙasashen biyu.

Sai dai gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce an fara tattauna batun shirya taron tun watanni da suka gabata, kuma Pretoria ta fahimci cewa Ghana na son ɗage taron ne lokacin da ta nemi tabbatar da shirye-shiryen gudanar da shi.

Mai magana da yawun Shugaba Ramaphosa, Vincent Magwenya, ya shaida cewa duk da jinkirin, ƙasashen biyu za su ci gaba da tattaunawa ta hanyoyin diflomasiyya domin cimma sabon lokacin da ya dace da ɓangarorin biyu.

Afirka ta Kudu ta sha fama da zanga-zangar adawa da baƙin haure a cikin watannin baya. Ko da yake wasu daga cikin zanga-zangar sun kasance cikin lumana, wasu lokuta sun rikiɗe zuwa tashin hankali, inda aka kai hare-hare kan baƙin ƙasashe tare da sace kayayyaki daga shagunan da ‘yan ƙasashen waje suka mallaka.

Gabanin ranar 30 ga Yuni, gwamnatin Ghana ta kwashe ɗaruruwan ‘yan ƙasarta daga Afirka ta Kudu bayan wata ƙungiyar da ke adawa da baƙin haure ta bai wa baƙin da ba su da takardun zama wa’adin su fice daga ƙasar.

Kwakye Ofosu ya jaddada cewa Ghana na mutunta dangantakarta da Afirka ta Kudu, amma ya ce zai fi dacewa Shugaba Ramaphosa ya kai ziyara Ghana ne bayan an shawo kan matsalar hare-haren ƙyamar baƙi, domin kada wannan batu ya mamaye muhimman tattaunawar da ake son yi.

A makon da ya gabata, Ma’aikatar Harkokin Wajen Ghana ta sanar da cewa wani ɗan ƙasar Ghana ya mutu bayan an harbe shi a yankin Khayelitsha da ke birnin Cape Town yayin zanga-zangar adawa da baƙin haure da aka yi ranar 30 ga Yuni.

Sai dai rundunar ‘yan sandan Afirka ta Kudu ta ce ba ta da wani rahoto da ke nuna cewa irin wannan kisan ya faru a wannan rana.

A cewar ‘yan sandan, gaskiya ne an kashe wani ɗan ƙasar Ghana a wani yankin Cape Town, amma hakan ya faru ne kwana ɗaya kafin ranar da Ghana ta ambata.

Sun kuma bayyana cewa binciken farko ya nuna kisan na da alaƙa da wata matsalar karɓar kuɗin fitina, ba wai hare-haren ƙyamar baƙi ba.

Duk da wannan saɓanin bayanai, jami’an diflomasiyya na ƙasashen biyu sun bayyana cewa za su ci gaba da tattaunawa domin tabbatar da cewa dangantakar Ghana da Afirka ta Kudu ba ta lalace ba sakamakon tashin hankalin da ake fuskanta.

By ukarofi

Leave a Reply