Wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta na wata mai sana’ar gashin masara da ta yi iƙirarin cewa tana samun sama da naira miliyan 2.5 a kowane wata ya jawo cece-kuce a tsakanin ‘yan Nijeriya, inda wasu suka nuna shakku kan iƙirarin, yayin da wasu kuma suka ce hakan na iya yiwuwa idan kasuwancin yana gudana a wuri mai kyau kuma ana tafiyar da shi yadda ya kamata.
A cikin gajeren bidiyon da ya karaɗe shafukan sada zumunta daban-daban, an ga wata mata tana tambayar mai sayar da masarar yawan kuɗin da take samu daga sana’arta.
Da amsa cikin kwarin gwiwa, ‘yar kasuwar ta ce: “A kowane wata ina samun kusan Naira miliyan 2.5.”
Sai dai har yanzu ba a tabbatar ko bidiyon wani wasan kwaikwayo ne da masu ƙirƙirar abubuwan intanet suka shirya ko kuma hira ce ta gaske da aka yi a kan titi ba. Duk da haka, iƙirarin ya bazu cikin sauri tare da jan hankalin jama’a.
Tun bayan yaɗuwar bidiyon, dubban mutane sun bayyana ra’ayoyinsu a shafukan sada zumunta irin su ɗ da Instagram. Ra’ayoyin sun kasu gida biyu, inda wasu suka ce adadin kuɗin da ta ambata ya yi yawa fiye da yadda ake zato, yayin da wasu suka dage cewa mai sana’ar masara na iya samun irin wannan kuɗin idan tana sayarwa a wurin da ke da yawan kwastomomi.
Wani mai amfani da shafin ɗ mai suna cipherbanks ya yi ƙoƙarin kare iƙirarin, yana mai cewa mutane da dama ba sa fahimtar yadda kasuwanci ke gudana.
Ya ce idan ana sayar da gasasshiyar masara kan naira 1,000 kowacce, kuma ana iya sayar da fiye da guda 100 zuwa 200 a rana, hakan na iya kai tallace-tallace sama da naira 100,000 a rana, wanda zai haura naira miliyan biyu a wata idan aka yi ciniki na kusan kwanaki 20 kacal. Ya kuma ƙara da cewa idan farashin kowacce masara ya kasance naira 500, sayar da guda 200 a rana ma zai iya samar da irin wannan kuɗin, musamman idan aka haɗa da sayar da gwanda da kwakwa da ake yi tare da masarar.
Sai dai wasu sun yi watsi da iƙirarin. Wata mai amfani da shafin mai suna @priye ta yi zargin cewa bidiyon wani nau’i ne na tallata manufofin jam’iyyar APC.
Shi kuwa stazzy_empire ya yi tsokaci da cewa, “Ga wadda ake cewa tana samun miliyan 2.5 a wata, amma har yanzu tana fama da rayuwa.”
A nasa ɓangaren, emoney__sniper ya yi mata fatan alheri, yana cewa idan da gaske tana samun irin wannan kuɗin daga kasuwancin, Allah Ya ci gaba da albarkace ta da wannan arziki.
Sai kuma princecyril5, wanda ya ce ba zai yiwu ba, yana mai cewa ko da ta sayar da masara guda 200 a rana kan naira 300 kowacce, har yanzu ba za ta kai adadin da ta ambata ba.
Har yanzu bidiyon na ci gaba da jawo martani, yayin da ake ci gaba da muhawara kan ko iƙirarin gaskiya ne ko kuma an yi shi ne domin jan hankali a kafafen sada zumunta.
