Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Tsohon Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Hon. Umar Haruna Doguwa, ya zama sabon Shugaban jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) a Jihar Kano.
An gudanar da zaɓensa ne a taron babban zaɓen jam’iyyar na jiha, wanda ya kammala a safiyar Laraba ƙarƙashin kulawar Kwamishinan Zaɓe na INEC a Kano, Ambasada Zango Abdu.
Wakilai daga ƙananan hukumomi 44 na jihar sun amince da Doguwa da sauran ‘yan takarar maslaha ta hanyar kaɗa ƙuri’ar murya, a wani tsari da majiyoyin jam’iyyar suka bayyana a matsayin mai cike da zaman lafiya da gaskiya.
An ware kujerar shugabancin ga Yankin Sanatan Kano ta Kudu, wanda shi ne yankin Doguwa, bisa tanadin dokokin jam’iyyar. Ya gaji Abdullahi Abbas, wanda ya shafe shekaru goma yana shugabancin jam’iyyar a jihar.
Doguwa, wanda ya taɓa shugabantar APC a lokacin wa’adi na biyu na tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi murabus daga mukaminsa na Kwamishinan Albarkatun Ruwa a majalisar Gwamna Abba Kabir Yusuf gabanin taron zaɓen, lamarin da ya nuna shirinsa na komawa shugabancin jam’iyya.
A jawabin bankwana nasa, tsohon shugaban jam’iyyar Abbas ya bayyana taron a matsayin “lokaci na farin ciki” ga jam’iyyar.
Ya gode wa ‘yan jam’iyya da shugabanni, ciki har da tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Gwamna Yusuf, bisa goyon bayan da suka ba shi a tsawon wa’adinsa.
Kazalika, ya nemi yafiya daga duk wanda ya ɓata wa rai, tare da kira ga mambobi su mara wa sabon shugabanci baya gaba ɗaya.
Da yake magana kan taron, Shugaban Kwamitin Gudanar da Taron na Jiha, Rabiu Suleiman Bichi, ya bayyana cewa wakilai 2,420 da aka tantance ne suka halarci zaɓen.
Ya jaddada cewa kasancewar jami’an INEC a wajen ya ƙara tabbatar da sahihancin tsarin.
A nasa ɓangaren, Doguwa ya nuna godiya tare da alƙawarin shugabanci mai haɗa kan kowa. Ya ce, “Na ji daɗin amincewar da wakilanmu da shugabannin jam’iyya suka nuna mini. Hankalina zai karkata ne wajen haɗa kan dukkan mambobi da ƙarfafa tsarinmu a faɗin Jihar Kano.”
Sauran shugabannin da aka tabbatar ta hanyar maslaha sun haɗa da: Salisu Majje Ahmed Gwangwazo a matsayin Mataimakin Shugaba; Farfesa Yusuf Mohammed a matsayin Sakataren Jiha; Nura Yaro a matsayin Mataimakin Sakatare; Abdul Adamu (SAN) a matsayin Mai Ba da Shawara kan Harkokin Shari’a; Bashir Yusuf a matsayin Mataimakin Mai Ba da Shawara kan Shari’a; Farouƙ Abdullahi Garo a matsayin Sakataren Kuɗi; Salisu Yahaya a matsayin Shugaban Matasa; Musadiƙ Wazari a matsayin Mataimakin Shugaban Matasa; Abubakar Salisu a matsayin Mai Binciken Kuɗi; da Hajiya Fatima Abdullahi Dala a matsayin Shugabar Mata, da sauransu.
An rantsar da sabbin shugabannin a gaban jagororin jam’iyya da masu ruwa da tsaki a wani biki da aka bayyana a matsayin “tarihi kuma mai haɗa kan jama’a.”
A jawabinsa, Gwamna Yusuf ya taya sabbin shugabannin murna tare da kira gare su da su tabbatar da amincewar da aka yi musu.
Ya ce, “Nasara da ci gaban wannan jam’iyya a Kano na dogara ne da ladabi, haɗin kai da jajircewa. Ina kira ga sabon shugabanci da su yi aiki tuƙuru domin cimma muradunmu.”
Ya kuma ƙarfafa musu gwiwa su ƙara ƙarfafa tsarin jam’iyyar da ciyar da manufofinta gaba a faɗin Jihar Kano gabanin zaɓen 2027.
