Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin jihar Neja ya bai wa masu riƙe da mukaman siyasa da masu riƙe da ofisoshin gwamnatin da ke tunanin tsayawa takara a zaben 2027 da su ajiye aikinsu kafin ko a ranar 23 ga watan Maris ɗin 2026.
Ko’odinetan yaɗa labarai na ofishin sakataren gwamnatin jihar Neja, Lawal Tanko, ne ya bayyana hakan a cikin wani jawabi a ranar Lahadi, inda ya kafa hujja da fitar da jadawalin zaɓe da hukumar INEC ta yi.
A cewar jawabin da sakataren gwamnatin jihar (SSG) ya fitar, Abubakar Usman, ya ce, umarnin ya zama dole domin tabbatar da an bi ka’idojin zaɓe da ya shafi masu sha’awar tsayawa takara.
INEC tun da fari ta sanar da jadawalin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da ‘yan majalisa a ranar 16 ga watan Janairun 2027 a yayin da za a yi zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jiha a ranar 6 ga watan Fabarairun 2027.
Hukumar ta sanya ranar 23 ga watan Afirilun 2026 domin fara zaɓukan cikin gida a fadin Nijeriya a shirye-shiryen tunkarar babban zaɓe.
Usman ya ce, akwai buƙatar masu riƙe da muƙamai da ke son tsayawa takara da su ajiye muƙamansu kamar yadda yake a tanadin doka.
“Ana sa ran fara zaɓukan cikin gida na jam’iyyu ne daga 23 ga watan Afirilun 2026,” ya bayyana.
“Sakamakon haka, ana shawartar dukkan jami’an gwamnati da su ajiye aikinsu nan da 23 ga watan Maris ɗin 2026 domin cika sharaɗin wata ɗaya na ajiye aiki kafin neman wani matsayi,” ya bayyana.
Sakataren gwamnatin ya ce, wannan umarni ya shafi dukkan masu riƙe da muƙamai siyasa da jami’an gwamnati waɗanda suke da burin tsayawa takara a kakar zaɓe mai zuwa.
Ya kuma ce bin wannan umarni zai tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta bi tanadin kundin tsarin mulkin Nijeriya da dokokin tsayawa takara.
Usman ya jaddada aniyar gwamnatin na bin ƙa’idoji da tabbatar cewa harkokin shari’a sun yi daidai da tanadin hukumar zaɓe ta ƙasa.
