Modu Mustapha ya yaba wa Gwamna Zulum kan ayyukan raya ƙasa

Spread the love

Daga GAMBO ISA a Abuja

Sakataren Dindindin na Ma’aikatar ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu ta Jihar Borno, Alhaji Modu Mustapha, ya yaba wa Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Baba Gana Umara Zulum, bisa ƙoƙarinsa na ci gaba da aiwatar da ayyukan raya ƙasa da kuma inganta shugabanci mai haɗa kan al’umma a faɗin jihar.

Modu Mustapha ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar, wadda aka rabawa jaridar Blueprint Manhaja, inda ya kuma nuna godiyarsa ga gwamnan bisa naɗin da ya yi masa a matsayin sakataren dindindin a ma’aikatar.

A cewarsa, gwamnatin Zulum ta samu gagarumin ci gaba a fannoni da dama, ciki har da bunƙasa jarin dan Adam, ayyukan more rayuwa, tsaro da kuma saurin sakin kudade ga ma’aikatun gwamnati da hukumominta domin gudanar da ayyuka.

Ya kuma yaba wa gwamnan bisa yadda yake samar da kudade a kan lokaci domin gudanar da ayyukan Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, wanda a cewarsa hakan na taimakawa wajen inganta ayyukan gwamnati a matakin kananan hukumomi.

Sakataren dindindin din ya kuma yi kira ga ma’aikatan gwamnati da su mara wa manufofin gwamnati baya tare da jajircewa wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata, tare da kauce wa rashin zuwa aiki ko jinkiri wajen halartar aiki.

Haka kuma ya bukaci ma’aikatan kananan hukumomi 27 na jihar da su rungumi manufofi da hangen nesan gwamnatin jihar domin tabbatar da kyakkyawan aiki da samar da ayyukan da za su amfani al’umma.

Modu Mustapha ya kara da cewa hangen nesan Gwamna Zulum na samar da ayyukan raya kasa a fadin kananan hukumomi 27 na jihar na daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen inganta rayuwar al’umma.

Ya kuma yaba wa gwamnatin jihar bisa shirye-shiryen horaswa da kara wa ma’aikatan gwamnati kwarewa, domin inganta ayyukan su da kuma kara ingancin hidimar da suke bayarwa ga jama’a.

A bangaren zaman lafiya, ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da inganta zaman lafiya da hadin kai, tare da ci gaba da yin addu’o’i domin samun nasara a yaki da matsalar ta’addanci da ke addabar yankin.

Sakataren dindindin din ya kuma yi kira ga matasa da mata da su dauki ilimi da muhimmanci, yana mai cewa ilimi shi ne ginshikin ci gaba da karfi a rayuwa, tare da gargadin su da su guji shaye-shayen miyagun kwayoyi.

A karshe, Alhaji Modu Mustapha ya bukaci al’umma, shugabannin al’umma, malamai, matasa, mata da ma’aikatan gwamnati da su ci gaba da bai wa manufofin gwamnati goyon baya, su kasance masu rikon amana da jajircewa wajen aikinsu, tare da ci gaba da addu’a domin cigaban Jihar Borno da Nijeriya baki daya.

By ukarofi