Yadda APC da ADC ke sabunta rajistar mambobinsu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Jam’iyyun siyasa a Nijeriya sun ƙara ƙaimi wajen sabinta rijartar mambobinsu yayin da wa’adin da aka gindaya domin kowacce ta miƙawa hukumar zaɓen ƙasar cikakkiyar rijistar ke kawo jiki.

Wannan na daga cikin shirye-shiryen tunkarar baban zaɓen ƙasar na 2027.

A ƙarƙashin sabon jaddawalin zaɓen da hukumar zaɓen Nijeriya, INEC ta fitar, ana buƙatar jam’iyyun siyasar ƙasar su gabatar da cikakkiyar rijistar mambobinsu ya zuwa ranar 2 ga watan Afirelun 2026.

Umarnin da INEC ta bai wa jam’iyyun siyasar na daga cikin tanadin dokar zaɓen Nijeriya ta 2026, wadda ke neman inganta yadda jam’iyyun siyasar ƙasar ke gudanar da harkokin su na cikin gida da kuma samar da tsari mai kyau na fitar da ‘yan takara a cikin jam’iyyun.

Wannan na zuwa ne yayin da wasu masu sharhi ke gnin cewa jam’iyyun na da ƙarancin kayan aiki na cika ƙa’idar hukumar zaɓe (INEC) wadda ke neman rijistar mambobin jam’iyyun siyasar ya zamo ta hanyar amfani da fasahar zamani, musamman ta la’akari da ƙurarren lokacin da aka ware domin wannan aiki.

Jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar ta ce ta fara aikin sabinta rijistar mambobin nata, wanda ta ce yaa gudana cikin nasara a dukkan mazaɓun ƙasar ciki harda na Abuja babban birnin Nijeriya.

Sanarwar da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar Feliɗ Moka ya wallafa a shafinta na ɗ, ta ce aikin zai samar da cikakkiyar rijistar mambobin APC na ƙasar, ya kuma tabbata jam’iyyar ta cika ƙa’idar shiga zaɓe mai zuwa.

Ya yi bayanin cewa tsaffin ‘ya’yan APC da kuma sabbi ne suka yi wannan rijista ta amfani da lambar katinsu na ‘yan ƙasa wato NIN.

APC ta ce wannan dama ce ga dukkan ‘yan Nijeriya da suka cika shekara 18 su shiga dama ta shiga a dama da su a fagen siyasar ƙasar, musamman a wannan lokaci da jam’iyyar ta ce tana aiwatar da sabon tsarin bunƙasa fahimtar juna tsakanin mambbinta.

Ita ma jam’iyyar adawa ta ADC ta soma rajistar inda a cikin wani bayani da ta fitar mai dauke da sa hannu sakataren watsa labaranta na ƙasa Bola Abdullahi, ta bayyana cewa ta fara aikin mambobinta ta hanyar latironi domin tunkarar manyan zabukan 2027 da ma na share fage a nan gaba kadan.

Jam’iyyar ta ce a yanzu haka dubban ‘ya’yanta a fadin Nijeriya na ci gaba da yin rajistar.

Jam’iyyar ta ADC da ke gaba-gaba a jam’iyyun adawar kasar ta bayyana cewa sai wadanda suka yi cikakkiyar rajista da ita kuma aka dauki bayanansu ne za su shiga zabukanta na share fage.

By ukarofi