Kungiyar Tsangaya ta naɗa Gwani Ibrahim a matsayin shugabanta na ƙasa

Spread the love

Daga WAKILINMU

Kungiyar Tsangaya da ke fafutukar samar da ci gaba ga malaman tsangaya da almajirai a faɗin Nijeriya, ta naɗa Gwani Ibrahim Mai Bindiga Hadejia a matsayin sabon Shugabanta na ƙasa.

An gudanar da bikin naɗin ne a yau Talata, 27 ga watan Janairu, a dakin taro na Naicon Luɗury Hotel da ke Abuja.

Taron ya samu halartar manyan shaihunnai da gwanayen Alƙur’ani mai girma daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Mahalarta taron sun bayyana naɗin a matsayin wani babban ci gaba ga harkokin ƙungiyar Tsangaya, suna masu cewa shugabancin Gwani Ibrahim Mai Bindiga zai samar wa almajirai dama da tallafi a matakai daban-daban.

Sun jaddada cewa manufar ƙungiyar a kullum ita ce fafutukar ganin an samar wa almajirai ‘yanci, ilimi mai amfani da kuma hanyoyin dogaro da kai, tare da gabatar da buƙatunsu ga gwamnatocin ƙasa.

A nasa jawabi, sabon Shugaban na ƙasa, Gwani Ibrahim Mai Bindiga, ya gode wa Allah bisa damar da aka ba shi, tare da yin alƙawarin yin aiki tuƙuru domin kawo ci gaba ga almajirai da malaman tsangaya a duk faɗin Nijeriya.

Hakazalika, ya buƙaci cikakken goyon baya daga mambobin ƙungiyar domin a haɗa kai wajen cimma manufofin da aka sa a gaba.

Naɗin Gwani Ibrahim Mai Bindiga ya biyo bayan kokarinsa da jajircewarsa a matsayin Shugaban Tsangaya na Jihar Jigawa, mukamin da ya rike tsawon shekaru tara, inda ya samar da gagarumin ci gaba a ɓangaren kula da harkokin tsangaya da almajirai.

By ukarofi